Connect with us

LABARAI

Sabon Shugaban Hukumar Alhazai Ta Katsina Suleiman Kuki Ya Shiga Ofis

Published

on

Sabon shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Katsina. Alhaji Suleiman Nuhu Kuki ya shiga ofis domin kama aiki kamar yadda doka ta tanada tare da fuskantar aiki gadan-gadan.

Tun da farko a jawabinsa a lokacin taron shigarsa ofis domin kama aiki, Suleiman Kuki ya fara mika godiyarsa ga Allah (SWA) wanda ya nuna masa wannan lokacin tare da mika sakon godiyarsa ga gwamna jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari da ya yi masa wannna nadi.

Haka kuma shugaban ya bayyana cewa ba shi wannan mukamai ba yana nufin ya fi kowa ba ne, dama ce da Allah ya bashi, kuma ana iya ba kowa domin Allah shi ne mai bayarwa.

Alhaji Suleiman Nuhu Kuki ya kara da cewa da yarda Allah wannan hukuma ta jin dadin alhzai zata amsa sunanta tare da yin aikin da yasa aka kafa ta, inda ya ce yana da tabbacin zai samu dukkanain taimakon da yake neman domin yin aiki yadda ya kamata.

Kazalika ya bayyana cewa akwai kalubale a gabansa saboda haka ya zama wajibi ya yi aiki tukuru domin sauke nauyin da ya rataya akan sa, yana mai cewa ya shirya tsaf domin kawo muhamman sauye-sauye a wannan hukuma.

Alhaji Suleiman Kuki wanda ya bada tabbacin cewa da yarda Allah wannan hukuma ta jin dadin alhazai ta jihar Katsina zata cigaba da yin zarra a wajan aikin Hajji duk shekara tare da hadin gwiwar sauran ma’aikata da masu ruwa da tsaki akan sha’anin aikin Hajji na jihar Katsina

“A matsayina na ma’aikacin gwamnati, ina sane da cewa ma’aikata su ne ginshikin samun nasarar aikin gwamnati, don haka ina kira ga ma’aikatan wannna hukum ta jin dadin alhazai da su zage damtse su bada cikakken hadin kai da goyon baya tare da aiki tukuru don darajar hukumar da ma’aitatan ta daukaka.” Inji shi

A karshe ya yi godiya ga dumbin jama’ar da suka nuna goyan bayan da aika masa da sakon fatan alheri akan wannan mukami da aka ba shi, yana mai rokonsu addu’a da zummar Allah ya ba shi ikon sauke wannan nauyi da ya rataya akansa da sauran ma’aikata.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: