Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Sabon VAT Da Tashin Farashi Ne Manyan Matsalolin Tattalin Arzikinmu – Binciken Cordros

Published

on

Binciken cibiyar Cordros ya ba da sanarwar cewa, sabon harajin da aka kara VAT da matsin lambar hauhawar farashin kayayyaki su ne manyan matsalolin da tattalin arzikin a Nijeriya.

Masu sharhi a Binciken Cordros sun bayyana wannan a cikin Rahoton tattalin arzikin mako-mako a aka fitar a karshen mako.

A ci gaban dai, manazarta sun ce: “Dangane da tsammaninmu ayyukan tattalin arziki a Nijeriya sun samu koma-baya kadan a cikin watan Janairu 2020, dangane da bukatu na jawo hankulan mutane wanda aka shaida a watan Disamba na shekarar 2019. Daidai yayin da PMI mai tarin yawa ya dage a yankin na fadada maki 59.4, ya yi girma a hankali da sauri da maki (-2.1 ) idan aka kwatanta da watan da ya gabata.

Matsakaicin ya samo asali ne daga duka masana’antu na PMI da maki (-1.6 zuwa maki 59.2) da PMI wadanda ba masana’antu ba da maki (-2.5 zuwa maki 59.6).

Tare da daidaitawa a cikin sabon umarni da maki (-1.8) da matakan samar da aiki da maki (-0.7). ” “ Yawan ci gaba da mayar da hannun jari daga hannun masu saka jari na kasashen waje da kuma sakamakon kwastomomin Nijeriya ya kasance nan da farkon 2020.

Ko da yake, dangane da watan Disamba 2019, durkushewar ba ta yi kasa sosai ba. Ya ce, wannan damuwarmu ta tsadar kudin kasar ta karkata ne daga abubuwan da aka sayar daga kadarorin na Naira zuwa farashin danyen mai.

Barkewar Cutar Coronabirus ta kwanan nan ta ci gaba da jefa tsoro a kasuwannin duniya, yayin da farashin Brent ya ragu da kashi 20.2 bisa 100 Shekara zuwa Yau, YTD zuwa USD54.93 kowace ganga, pb (6 ga Fabrairu 2019).

A ci gaba da barkewar kwayar cutar, ya wajaba a gare mu mu tilasta Babban Bankin Nijeriya, CBN sake tunani game da dabarun gudanar da harkokin waje, FD. Don haka, mun dauki yanayin mafi munin yanayin Dala 50 a kowace ganga, dangane da wannan, FD ajiyar za ta ragu zuwa Dala biliyan 3030.36 ta rabi na farko, H1-20. A nesa da hada-hadar kudade, da hanzarta dawo da martabar babban birnin kasar, domin kuwa sake fuskantar barazanar kai hare-hare kan darajar Naira zai tilasta Babban Bankin ya jefa shakku a cikin tunaninmu. ”In ji rahoton.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: