Connect with us

LABARAI

Sanata Wamakko Ya Kaddamar Da Rabon Tallafin Miliyan 317 Ga Marayu

Published

on

Shugaban kwamitin harkokin tsaro, kuma Mataimakin Shugaban kwamitin yaki da cin hanci, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya kaddamar da rabon tallafi ga marayu, wanda ya kai ma Naira Miliyan 317.7 domin raba wa marayu su 1,176 karkashin kungiyar bayar da tallafin musulunci ta (Islamic Relief Organization).

Wadanda suka amfana da shiri, sun hada da maza da mata, da suka fito daga Kananan Hukumomi 23 na Jihar Sakkwato.

Da yake jawabi a wajen taron, Sanata Aliyu Magatarda Wamakko, wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar Sanatocin Arewacin tarayyar Nijeriya, ya ce an fara wannan shirin ne da tantance marayu a shekarar 2009.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Sanatan a kan harkokin yada labarai, Bashir Rabe Mani Dan Masanin Mani ya Sanya wa hannu, ya raba wa manema labarai.

Sanata Wamakko, wanda ke wakiltar mazabar Sakkwato ta Arewa ya samu wakilcin Tsohon Ministan harkokin sufuri, Alhaji Yusuf Suleiman, inda ya kara da cewa, “wannan kungiyar sananniya ce da ta dade tana irin wannan aikin da kuma yin aikace-aikace, gine-gine a cikin Jihar.

Ayyukan sun hada da gina makarantun Islamiyya, gina masallatai da kuma bayar da taimako ga mabukata ta fuskoki daban-daban,” in ji shi.

Ya ci gaba da bayyana cewa, “don haka ne kungiyar ta taso domin bayar da tallafin yin karatu ga wadannan marayu, wanda zai taimaka wa marayun su ci gaba da karatunsu a fannonin da suka zaba”.

“Wannan an yi shi ne domin su ma su sami ilimi, wanda hakan zai ba su damar dogaro da kansu ta yadda za su amfani al’umma,” ya ce.

Sanata Wamakko ya kuma yi kira ga masu kula da marayun da suka amfana da su ji tsoron Allah ta fuskar yin amfani da abin da aka ba su kamar yadda ya dace, su yi amfani da shi kamar yadda aka tsara.

Ya kuma kara da fadakar da cewa “ku tuna fa za mu yi bayanin dukkan abin da muka aikata a ranar gobe kiyama.”

Ya kuma yi kira ga daukacin al’umma baki daya da su yi amfani da dukkan abin da suke da shi wajen taimaka wa marayu, Zawarawa da masu karamin karfin da ke cikin al’umma.

Ya ce, “domin babu wani abin da mutum zai bayar da ke da kankanta ko kuma yawa, in dai za a ba marasa galihu a cikin jama’a domin Allah”.

Sanata Wamakko ya kuma yi jinjina ga kungiyar da ke kasar Saudiyya bisa irin abubuwan da suke yi wa jama’a na aikace-aikace a Jihar Sakkwato.

Ya kuma yi kira ga kungiyar da kada ta gajiya wajen irin ayyukan da suke gudanarwa, musamman irin yadda ya kara rokon su da su kara yi wa Jihar Sakkwato, wadansu ayyukan.

A ta bakin wakilin kungiyar Huzaifa Tahir cewa ya yi wannan tallafin na shekarun 2011, 2012 da shekarar 2013 ne.

Kamar yadda ya bayyana cewa na shekarar 2014, za a rama shi a nan gaba kadan.

A nasa jawabin, Bako mai jawabi, Sheikh Yahuza Shehu Tambuwal, Limamin masallacin Juma’a na Uthman Bin Affan Sakkwato, kira ya yi ga daukacin jama’a da su taimaka wa marayu kamar yadda aka bukaci kowa a cikin musulunci.

Dukkan wadanda su ka yi jawabi a wurin taron sun yi godiya ga Sanata Wamakko da ya kawo wannan kungiya a Jihar Sakkwato a lokacin da ya ke Gwamnan Jihar, Sun kuma Jinjina wa kungiyar bisa abin da take aiwatarwa.

Da yake magana a madadin wadanda suka amfana, Ahmad Umar da Safiya Babuga, sun gode wa Sanata Wamakko da kuma kungiyar bisa abin da suka yi, wanda hakika zai kara bunkasa harkar iliminsu baki daya.

Sun kuma yi alkawarin yin amfani da kudin kamar yadda a ka bayar domin yi.

An dai bayar da mafi karamin kudi ga wadanda su ka amfana na Naira Dubu 200,000 mafi yawa kuma Naira Dubu 400,000.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: