Connect with us

RAHOTANNI

Shugaban Gudanarwa Na LEADERSHIP A YAU Ya Ziyarci Gidajen Rediyo A Kano

Published

on

A kokarinta na bunkasa harkokin sadarwa da kara karfafa dankon zumunci, LEADERSHIP A YAU ta ziyarci wasu Gidan Rediyo da ke, wadanda suka hada  Pyramid, Aminci da kuma Guarantee, bisa jagorancin Babban jami’inta, Malam Musa Muhammad tare da rakiyar Editan shiyyar Kano na Jaridar, Sani Anwar, Babban Wakilin Jaridar a Kano, Malam Abdullahi Sheka da kuma takwaransa, Haruna Akarada.

Tawagar ta fara isa Gidan Rediyon Pyramid ne, inda ta samu kyakkyawar tarba daga wurin Ma’aikatanta, bisa jagorancin Shugabanta na Jihar Kano, Malam Isma’ila Ahmad Dabai, tare da tattauna wasu muhimman batutuwa, wadanda suka hada da karfafa zumunci ta hanyar rika tallata juna tsakanin Gidan Rediyon da kuma Jaridar ta LEADERSHIP A Yau.

Har ila yau, Shugaban Gidan Rediyon ya bada tabbacin baiwa Jaridar fifiko, musamman wajen sharhin labarai da sauran makamantansu, sakamakon ganin ita ce Jarida ta Hausa kwallin-kwal da ke fitowa a kowace rana, ba ma a Nijeriya kadai ba, a duniya baki daya duk kuwa da irin tasirin da yaren Hausar ke da shi.

A karshe, kakafen guda biyu sun cimma kwakkwarar matsaya, domin kuwa shi ma Babban Shugaban Gudanarwa na LEADERSHIP A Yau, ya sha alwashin baiwa wannan Gidan Rediyo wani gurbi na musamman a farkon shafi ko bangon wannan Jarida, wanda ke nuna alama ko tambari, tare da lambobin da idan aka danna, ba tare da shan wata wuya ba, za a kama wannan Gidan Rediyo mai albarka.

Wanda ya ce wannan shiri nasa zai taimaka wajen kara sanar da jama’a yadda za a iya kama tashar, domin kuwa akwai mutane da dama da ke son rika sauraron ire-iren wadannan Gidajen Rediyo, amma ba su san yadda za su yi su kamo su ba.

Da yake mayar da matani, Shugaban gidan rediyon na Pyramid, Malam Isma’ila Ahmad Dabai ya nuna matukar godiyarsa da wannan ziyara, inda ya bayyana cewa dama can akwai sanayya tsakaninsa da Malam Musa Muhammad.

Malam Dabai ya kuma bayyana cewa babu shakka jaridar LEADERSHIP A Yau ta cancanci yabo, musamman bisa kafa tarihin da ta yi na kasancewa daya tilo da ta fara fitowa kullum cikin jaridun Hausa.

Daga nan ya bayyana amincewarsa da hadakar ‘ba ni Kanwa in ba ka Manda;’ wanda ya ce yin haka zai taimaka waje amfanar juna. Nan ta ce kuma ya nemi a kawo abin da za su rinka fada a kan jaridar, su kuma su bayar da alaminsu don a fara wannan shiri.

Daga nan ne kuma, sai tawagar ta LEADERSHIP A Yau wuce zuwa Gidan Rediyo na Guarantee, inda ta iske Manajan Darakta na gidan, wato Ahmad Tijjani Lawan, ta kuma yi katarin tattauna muhimman al’amura, wadanda za su taimaka wa wadannan kafafen sadarwa guda guda.

Haka zalika, daga cikin wadannan muhimman batutuwa da aka tattauna, sun hada da hanyoyin da za a bi a kulla kyakkyawan zumunci tare da yin kawance domin taimaka wa juna ta hanyar tallatawa. Duk dai da cewa, a fadin Nijeriya kaf babu inda ake sayen Jaridar LEADERSHIP A Yau kamar Jihar Kano, amma wannan ba zai hana a sake tallata ta ba, musamman ganin yadda ita ce Jarida daya tilo da ke fitowa a kullum a cikin jaridun Hausa.

Akwai yiwuwar duk wanda ke zaune a Kano ya santa, amma kuma bai san cewa kullum take fitowa ba, haka nan shi ma wannan Gidan Rediyo na Guarantee, wasu sun san shi, amma ba su san hanyar da za su bi su kamo shi ba. Don haka, ko shakka babu wannan zumunci ko kawance zai taimaka wa dukkanin kafafen guda biyu.

Amma sai dai shi Manajan Daraktan ya nemi a rubuto takarda ta musamman don neman wannan hadaka, wacce ya ce za su amince da ita ba tare da bata lokaci ba.

Wani abin ban sha’awa shi ne, Gidan Rediyon Aminci wanda wannan babbar tawaga ta ziyarta a karshe, shi ma ya yi irin wadannan alkawuran da sauran takwarorinsa suka yi, bisa jagorancin Malam Abubakar Galadanci mai aiwatar da shirin ‘Idon Mikiya’, a madadin Shugabar Gidan Rediyon, Hajiya Halima Aminu Wali.

Har wa yau, wannan Gidan Rediyo na Aminci, a nan take ya shirya wata kwarya-kwaryar tattaunawa (Interbiew) da Babban wannan Shugaban Gudanarwa na LEADERSHIP A Yau, wanda Karibu Na Madobi ya gudanar, don jin musabbabin wannan ziyara tasu da kuma wasu muhimman batutuwa kamar haka: “mun kawo wannan ziyara ne domin karfafa dakon zumunci a tsakaninmu da gidan Rediyon aminci, wanda kuma tun daga irin tarbar da muka samu, ya sa na samu natsuwar cewa an yi na’am da ita.”

Haka kuma cikin tattaunawar, Malam Musa Muhammad ya bayyana matukar jin dadinsa da jin cewa gidan rediyon Aminci suna daukar labarai daga jaridar ta LEADERSHIP A Yau , kuma suna ba su girmansu na cewa daga jaridar ce suka tsamo duk labarin da suka watsa. “Wannan ya sa na ji dadi matuka, tare da fatan za a ci gaba da haka,” in ji shugaban sashen.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: