Connect with us

RIGAR 'YANCI

Tsaro: Allah Zai Maganta Idan Dan kasa Ya Gyara Halinsa – Dr. Abdullahi

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’ar Bosso Estate da ke Minna, Dakta Umar Faruk Abdullahi, ya bayyana cewar, Nijetriya na iya komawa kamar yadda ta ke a shekarun baya muddin al’umma ta amince da gyara kurakurenta.

Ya ce, “idan an koma baya kamar irin lokacinsu marigayi Sardauna har lokacin su Marigayi Shehu Shagari kasar nan ta na zaune lafiya bisa fahimta da soyayyar juna, amma yanzu Allah ya canja mana yanayi, ya yi ma na irin na mutanen saba’i, ya yi ma na ni’imomi, amma mu ka butulce ba mu gode masa ba, sai ya canja mana wannan da azaba yanzu.”

Malam ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai bayan kammala sallar juma’a a harabar masallacin.

Ya cigaba da cewar, “wannan matsalar da ake ciki a yau na rashin zaman lafiya, da rashin wadatuwar arziki, rashin natsuwa da rashin zaman lafiya, dukkan hannayen mu ne ya janyo hakan. Allah ba zai canja ba, dole sai in mun canja.

“Saboda haka kowa ya tuba mu roki Allah gafara, mu nemi rahamar shi zai yafe muna kuma zamu samu karuwar arziki. Wannan matsalar da muke ciki a yau ba laifin shugaban kasa ba ne kuma ba na gwamnoni ba ne, dukkanmu mu tuba mu koma gare shi.

“Zina ta yi yawa, shan giya ta yi yawa, kisan kai ta yi yawa. Ina kira ga masu garkuwa da mutane da su tuba su gyara, su daina kashe mutane, Allah yana kishin bayinsa, in har ba mun bar wadannan miyagun halayen ba ne to ba ranar da zamu samu zaman lafiya a kasar nan. Duk yadda za a yi arzikin kasar nan ba zai dawo ba, domin kashe rai daya a wurin Allah na mumini yafi gaba daya a tarwatsa duniya, hadisi ya nuna kashe rai na mumini a wurin Allah yafi akan rushe dakin Allah.

“Gaya nan a kullun sai an yi kisa a kasar nan ba iyaka, dan haka wajibi ne idan har muna son Allah ya dube mu ya tausaya mana to wajibi ne mu tuba mu komawa Allah, ba abinda shugabannin kasar nan zasu iya yi kan kawo karshen wannan al’amari har sai mun komawa Allah.”

Dokta Umar ya jawo hankalin al’umma kan zama ana zagin shugabannin da kokarin daura masu laifi dan gane da sukurkucewar tsaro da cewar an bar gangane a na bugun taiki, domin mun bar Allah ne shi yasa Allah ya jarabce mu da wannan halin da mu ke ciki a kasar nan.

“Wajibi kowa ya ji tsoron Allah, mu gyara mu’amalar mu da shi, kowa yasan laifin sa kowa kuma yasan abinda ya dace, bai yiwuwa al’umma ta dauki zina kawa, ta dauki luwadi da yiwa kananan yara fyade a matsayin kawa da hanyar neman duniya sannan mu yi tsammanin samun rahamar Allah.

Mu talakawa mu ji tsoron Allah mu gyara mu’amala a tsakanin mu, shugabannin su ji tsoron Allah su kiyaye amanar da aka ba su, mu inganta tarbiyar ‘yayan mu, mu san kishin kasar mu a zukatan mu, kowa yayi kokarin sauke nauyin da ke kansa, Allah zai tausaya mana, zai ba mu mafita a wannan halin kuncin rayuwar da muke ciki a kasar nan,” inji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: