Connect with us

LABARAI

Yanzu-yanzu: Buhari Ya Kai Ziyara Maiduguri

Published

on

Shugaban kasa, Mohammadu Buhari ya sauka birnin Maidugurin jihar Borno, don bayyana alhini tare da jajanta wa jama’ar jihar kan harin da wasu mahara suka kai ranar Lahadi a kauyen Auno, a jihar.

Mista Buhari ya sauka Maidugurin ne kai tsaye daga kasar Ethiopia, inda ya halarci babban taron African Union Summit.

Ana sa ran ayarin tawagar tasa za ta fara yada zango a fadar Shehun Borno inda zai jajanta wa jama’ar jihar kana da gwamnatin jihar kan harin, wanda ya yi dalilin sakwantar rayukan jama’a da dukiyoyi.

Bugu da kari kuma, daga nan ne tawagar shugaban kasar za ta rankaya zuwa fadar gwamnatin jihar- gidan gwamnatin jihar Borno tare da mai masaukin sa, Gwamna Babagana Zulum.

Haka zalika kuma, ba a bayyana ko shugaban kasar ya ziyarci kauyen Auno, inda aka kai harin, ko ya ya.

Amma wata majiya ta tsegunta cewa, “Akwai yuwuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci Auno, duk da babu tabbacin ko jami’an tsaro za su bari ya kai ziyara a garin”.

A hannu guda kuma, gwamnan jihar Borno ne, Farfesa Babagana Zulum ne ya tarbi isowar shugaban kasar a filin jirgin saman Maiduguri.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: