Connect with us

LABARAI

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Biya Sowore Naira Dubu 200

Published

on

Babban kotun tarayya dake Abuja a ranar Laraba ta nemi Babban mai shigar da kara na gwamnatin tarayya, Abubakar Malami da su biya naira dubu dari biyu bisa abin da kotun ta kira “bata lokaci wajen gabatar da karar Omoyele Sowore.”

Sowore da kuma Olawale Bakare, ana zarginsu ne da zarge-zarge guda bakwai ciki kuwa har da na cin amanar kasa, zagin shugaban kasa Buhari da sauran su.

Sowore da Bakare DSS sun cafke su ne a ranar 3 ga watan Agusta bisa zarginsu da shirya zanga-zangar nan ta #RevolutionNow.

A ranar 6 ga watan Disamban 2019, SSS suka sake kama Sowore a gaban kotun tarayya a Abuja kwana daya da sakinsa daga wurin SSS din. Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ne ya saki Sowore da Bakare bayan sun shafe kwana 124 a wurin SSS.

Sai dai kuma a ranar 24 ga watan Disamban 2019, aka sake sakin Sowore.

Daga cikin wadanda suka halarci shari’ar ta yau sun hada da Farfesa Wole Soyinka, tsohon Sanata Shehu Sani, da kuma tsohon shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa (NHRC), Chidi Odinkalu.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: