Connect with us

RIGAR 'YANCI

Za Mu Dauki Nauyin Karatun ’Ya’yan Nakasassu 100 – Gwamna Matawalle

Published

on

Gwamnan Jihar Zamafara, Hon. Bello  Matawalen Maradun ya tabbatar da cewa ‘ gwamnatinsa zata dauki nauyin karatun ‘yan ‘yan Nakasasu dari da ke Jihar zawa jami’oin Kasara nan.

Gwamna Matawalen Maradun ya bayyana haka ne a loakacin taron da ya yi da nakasasun a gidan gwnatin da ke Gusau.

Hon. Muhammad Bello, Matawalen Maradun, ya bayyana takaicinsa na tura sama da dalibai 200 karatu wajen kasar, amma babu ‘ya’yan nakasasu ko daya, “alhali kuwa mun ce a zabo dalibai marasa galihu, sai ba a yi haka ba. Don haka wannamn gwamnatin taku ce nakasasu. Za mu tura ‘ya’yanku 100 zuwa jami’o’i, don su ma su sama karatu ingantace kamar sauran yara masu galihu.

“Kuma ita nakasa Allah ne ke jarrabar bawansa da ita. Don haka ni ma kaina Allah na iya rabata ta. Don haka dole ne mu kula da ku kuma mu shiga cikin lamuranku. Duk wanda ya taimaki nakasashe, Allah zai taimake sa,” in ji shi.

Gwamna Matawalen Maradun a nan take ya bai wa shugabannin kungiyar nakasasu motoci 10 da kuma Naira miliyan 10 ga sauran nakasasun.

Gwamna Matawalen Maradun ya kuma dau alwashin gyara cibiyar koyan sana’o’i ta nakasasun dan ganin sun iya sana’ar hannu dan dogaro da kansu.

A nasu jawaban sasan shuagabannin Nakasasun,Alhaji Shehu S.Fada,shuagaban Sarkin Kutare na Jihar Zamfara da Sarkin Makafi,Abubakar Keta da Alhaji Ibrahim Sani Bakura Sarkin Gurago da Sarkin Kuramai Malam Muhammad Umar,sun bayyyan wa gwamna Matawalen Maradun matsalolin su kuma anan ta ke ya tabbatar masu da cewa zai biya masu bukatun na su.

A karshe sun nika godiyar su ga gwamna Bello Matawalen Maradun akan karamcin da yayi masu na tura ‘ya ‘yansu karatu da fatan Allah ya kare gwamnatin sa daga Sharin makiya amin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: