Connect with us

LABARAI

An Cafke Karuwai 34 A Jigawa

Published

on

Jami’an hukumar Hisbah a Jihar Jigawa sun kama mata 34 da su ke tuhuma da aikata karuwanci, sa’ilin kuma da suka kwace kwalaben giya 147 a karamar hukumar Kazaure, ta Jihar.

Kwamnadan hukumar ta Hisbah a Jihar, Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana hakan cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai jiya a garin Dutse. Ya bayyana cewa an kama matan da ake tuhumar ne a wani farmaki da jami’an hukumar na shi suka kai a Unguwar Gada, da ke Kazaure.

Ya ce: “Yau din nan da misalin karfe 5 na safiya, jami’an mu sun kai wani farmaki a mahadar nan da ta shahara ta Gada, da ke karamar hukumar Kazaure.

“A lokacin farmakin an kama mata 34 da ake tuhuma da karuwanci da kuma maza guda 3 a bisa zargin su da aikata rashin da’a.”

Dahiru ya kuma bayyana cewa, a lokacin farmakin jami’an hukumar sun kuma kama kwalaben giya guda 147 da kuma buhu guda na kwalaben giyan wadanda babu komai a cikin su.

Kwamandan ya kara da cewa, jami’an na shi sun kuma kama wani da suke tuhuma da mallakan gwangwanayen giya guda 94 a irin wannan farmakin da suka kai a karamar hukumar Jahun, ta Jihar.

A cewar sa, duk an gurfanar da mutanan da ake tuhuma din a gaban babbar kotun Shwari’ar Musulunci da ke Kazaure.

Kwamandan ya kuma shawarci al’umma da su guji aikata munanan dabi’u, ya kara da cewa hukumar na shi ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin da ta ke yi na hana saye da sayar da giya da duk makamantan munanan halaye a cikin Jihar.

“Muna yin amfani da wannan kafar domin tunatar da al’umma cewa an fa haramta sha da siyar da giya a cikin wannan Jihar.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: