Connect with us

WASANNI

An Kammala Zangon Farko Na Firimiyar Nijeriya

Published

on

A karshen makon daya gabata ne aka karkare karawar zangon farko a gasar cin kofin Firimiyar Najeriya, wadda aka yi wasanni 19 duk da cewa da farko ba’a fara buga gasar da wuri ba sakamakon tsaikon gasar cin kofin nahiyar Africa.

Yadda kungiyoyi ke zuwa waje su ci wasa ya karawa gasar bana armashi, ganin an yi nasara a wasanni 23 a waje saboda a kakar wasa ta 2015 aka kafa tarihin cin wasanni 31 da kungiyoyi suka je suka ci wasanninsu, amma a zangon farko kuma nasara 19 kungiyoyin waje suka samu.

Kungiyar Dakkada ita ce tilo da ta yi rashin nasara a wasa daya a waje a bana, shi ne wanda ta yi da Mountain of Fire haka kuma a kalla kungiyoyi 15 sun ci wasa daya ko biyu a waje, bayan da aka kammala zangon farko.

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi wasan Firimiya 13 a jere ba tare da an doke ta ba, sai a karawar mako na 19 ta sha kashi a hannun kungiyar kwallon kafa ta MFM da ci 3-1 a jihar Legas.

Sannan kuma wani bincike ya fayyace cewar kungiyar da take ta daya a zangon farko ita ce ke lashe kofin inda aka ci takwas daga 10 a baya masu jan ragamar teburi kuma Lobi Stars ce ta daya kawo yanzu da maki 35, sai Plateau United ta biyu mai maki 33, yayin da Ribers United mai maki 32 ita ce ta uku a teburin.

Wadanda suke kasan teburi su hudu kuwa sun hada da Jigawa Golden Stars ta 17 mai wasa 18 da maki 20 sannan Rangers ce ta 18 mai kwantan wasa biyar da maki 17, ita ma Adamawa United maki 17 ne da ita a mataki na 19 sai kuma Nasarawa United a mataki na karshe ta 20 mai kwantan wasa daya da maki 16.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: