Connect with us

LABARAI

An Rantsar Da Shugabannin Kungiyar ‘Yan Kasuwa 13 A Jihar Nasarawa

Published

on

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta rantsar da shugabannin kungiyoyi 13 wadanda za su rinka sa ido a kan harkokin kasuwanci a jihar Nasarawa. Gwamnatin ta ce dai mutanen za su rinka aiki ne don ganin harkar kasuwanci ya habaka a cikin Jihar.

Da ya ke jawabi wajen taron bunkasa harkokin kasuwanci wanda ya gudana  a zauren taro na Ta’al da ke garin Lafia. Babban bako a wajen taron, Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce; babu abin da ya kai harkan kasuwanci mahimmanci a cikin al’umma. Ya ce; harkan kasuwanci kowa za ka tarar yana kokarin tabawa.

Manyan ma’aikatan Gwamnati da ‘yan siyasa da ma mata masu zaman gida. Ya ce; harka ne mai albarka, za ka ga an tashi daga wata kasa zuwa wata kasa domin gudanar da harkan kasuwanci.

Babu abin da zai daga darajar kasar mu da manyan birane face kasuwanci.

Ya yi kira ga al’umman Jihar Nasarawa da su rungumi harkan kasuwanci saboda yana daga darajar gari. Sannan ya yi kira ga matasa maza da mata, da ka da mutum ya rena sana’ar da yake yi saboda wannan shi ne martabar shi.

Lokacin da ya ke  bayani gaban dubban al’umma da suka hada har da mataimakin Shugaban kasa, Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule (Barayan Lafia) ya ce, harkan kasuwanci harkace da take habaka kasa baki-daya.

Saboda ta hanyar kasuwanci ne kowace Gwamnati take samun kudaden shiga da take yi wa jama’a aiki na raya kasa.

Kowace kasa tana alfahari da hanyoyin kasuwanci da al’umman ta ke gudanarwa. Gwamnan ya kara da cewa, akwai hanyoyi da dama da Jihar Nasarawa za ta bunkasa ta fuskacin kasuwanci.

Hanyoyin hakar ma’adinai da suke karkashin kasa zai iya gina Jihar Nasarawa, ta harkan ci gaban kasuwanci. Jihar tana da albarkatun kasa mai tarin yawa wanda idan aka samu damar yin mu’amala da ‘yan kasuwa za su sarrafa abubuwa da dama.

Al’umman Jihar Nasarawa maza da mata suna da rawar da za su taka a harkokin kasuwanci. Musamman masu kananan sana’o’in da ma manyan ‘yan kasuwa da masu sarrafa kayayyakin gona ta hanyar gudanar da abinci na gida.

Gwamnan ya yi kira ga masu gudanar da kananan sana’o’i da su zage damtse wajen gudanar da ayyukansu, saboda gaba za su yi murna da farin ciki.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: