Connect with us

NOMA

Anchor Borrowers: Ba Mu Kai Karar Manoma 70,000 Kotu Ba, Cewar CBN

Published

on

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da cewa, bai kai karar manomi ko daya gaban kotu ba a cikin wadanda su ka ci bashin bankin, don yin noma.

Bankin ya na mayar da martani ne kan rahoton da wata jarida ta wallafa cewar, Babban Bankin na Nijeriya (CBN) ya maka manoman da su ka ci bashin bankin a karkashin shirin nan na aiikin noma mai lakabin Anchor Borrowers su ka kuma ki biya.

Mai magana da ywaun babban bankin na Nijeriya CBN Mista Isaac Okorafor ne ya sanar da hakan a cikin wata sanatwa da ya fitar a babban birnin tarayyar Abuja.

Idan za a iya tunawa, Jaridar Daily Trust ta ruwaito Shugaban kungiyar manoman Shinkafa na Jihar Kebbi, Muhammed Augie, ya ce har yau wadanda suka ci bashin CBN tun a cikin 2015, su 70,000 ba su biya bashin ba.

Bugu da kari, an kuma ruwaito Shugaba Augie ya na cewa manoma 200 ne kacal daga cikin 70,000 wadanda suka ci lamunin suka biya na su a Jihar Kebbi.

Shugaba Augie ya ci gaba da cewa, kafin a bayar da lamunin ana manoman Shinkafar a jihar suna noma tan-tan na Shinkafar guda 70,000, inda ya kara da cewa, amma bayan sunci bashin, lamunin na naira bilyan 17, an rika noma har tan na shinkafa milyan 1.6.

Shugaban ya yi nuni da cewa, duk da haka amma karbo bashin ya zama jekala-jekala, inda ya kara da cewa, sai da mu ka hada kotuna, inda ya sanar da cewa, yanzu duk kotunan Majistare da ke a Kebbi za ka ga mun maka manoman da suka ji biyan kudin a can kuma har zuwa yau, mutum 200 kacal basu maido da bashinnna bankin ba.

Kakainnna CBN, Okorafor ya ce naira bilyan 16 ne aka raba a Jihar Kebbi, ba bilyan 17 ba, inda ya kara da cewa Kuma duk an karbi kudaden, sauran da ba a kai ga karba ba, naira bilyan 2.6 ne suka rage a hannun manoma.

Kakakin ya yi nuninda cewa, maimakon a kai manoma kotu domin su biya kudaden , sai aka amince CBN ta kara wa manoman wa’adin lokacin biyan basussukan.

Wani da ba ya son a bayyana sunan sa, ya karyata kakakin Okorafor, inda ya ce, an kai manoma da yawa kotu, kuma su na ta kokarin ganin sun biya.

An ruwaito cewa, ana zargin manoman sun cinye kudaden da bababban bankin na CBN ya basu bashin ne.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: