Connect with us

LABARAI

Ba Mu Wulakanta Mai Tattakin Kwankwasiyya Ba, Inji Ibrahim Adam

Published

on

Daya daga cikin masu taimakawa Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin tutar jam’iyar PDP, Abba Kabir Yusif, mai suna Ibrahim Adam, ya bayyana cewa basu waulakanta kwamared  Aminu Tanko ba, mutumin jihar Katsina wanda yayi tattaki daga jihar zuwa Kano domin jajantawa ‘yan Kwankwasiyya alhinin hukuncin da kotun koli ta yanke, inda ta kori karar ta Abba Gida-Gida da jam’iyyar PDP.

 

A ranar 9 ga watannan ne dai wasu jaridu suka ruwaito cewa tsagin kwankwasiyya sun wulakanta matafiyin, wanda yayi tattakin saboda su inda kuma hotunansa suka dinga yawo a kafafen yada labarai na zamani.

 

Ibrahim ya ce, sunyi farin ciki da murna da nuna kulawa da kwamared Aminu Tanko yayi musu bisa hukuncin kotun wadda har tasa yayi tattaki daga jihar Katsina zuwa Kano domin jajantawa jagoran Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da dan takarar jam’iyyar Abba Kabir Yusuf da mutanen jihar Kano sannan kuma suna kira ga al’umma kwamaret Aminu bai sanar dasu cewa zaiyi tafiyar ba wanda hakan yasa shugabannin nasu suka bar jihar domin wasu harkokin a wajen jihar.

 

“Gaba daya tun daga kan Kwankwaso da Abba K. Yusuf da ragowar masu fada aji a tsagin na kwankwasiyya suna Abuja lokacin da mutumin yazo amma duk da haka wasu daga cikin ‘yan uwa sun karbe shi hannu bibbiyu wanda hakan yake nufin duk da haka an nuna masa kara kuma anyi maraba dashi” in ji Ibrahim

 

Ya ci gaba da cewa “ Duk da cewa muna farin ciki da irin kulawar da Aminu ya nuna kuma muna kira ga magoya bayanmu dake fadin kasar nan da kada su cigaba da irin wannan tattaki mai cike da hatsari duba da irin halin rashin tsaron da ake ciki a kasar nan sannan kuma tafiyar zata iya haifar da matsalar lafiya ga masu yinta”

 

Ya kara da cewa “Muna maraba da irin addu’o’in da magoya baya sukeyi kuma muna da yakinin cewa Allah SWT zai amsa addu’o’in mu bayan zalincin da akayi mana a kotu sannan kuma muna sake jinjina ga kwamaret kuma muna fatan zai samu lokaci domin ganawa da shugabannin mu idan sun dawo Kano.

 

A karshe, Ibrahim ya jinjinawa gaba daya magoya bayan Kwanlwasiyya bisa goyon bayan da suke yiwa tafiyar da kuma zalincin da akayi musu a kasar nan

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: