Connect with us

JAKAR MAGORI

Budurwa Ta Kashe Jaririnta Ta Barne A Daji

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Jigawa ta cafke wata budurwa mai suna Hauwa Sani ‘yar shekara 18 da haihuwa, bisa laifin kashe jaririnta sabon haihuwa a kauyen Dabi da ke cikin karamar hukumar Ringim.

Kakakin rundunar jihar, SP Abdu Jinjiri shi ya tabbatar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Dutse. Ya bayyana cewa, an kama matar ne bayan wasu daga cikin mazauna kauyen sun sanar wa ‘yan sanda cewa, Hauwa ta haifi yaro na miji ba tare da aure ba, amma ba a san inda jaririn yake ba. Jinjiri ya kara da cewa, lokacin da ‘yan sanda suka sami wannan labarin, nan take suka kama matar. Ya ce, lokacin da aka tuhume ta, wacce ake zargin ta amsa cewa ta kashe jaririn sannan ta haka rami ta barne shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ci gaba da cewa, wacce ake zargin ta bayyana cewa, ta aikata wannan laifin ne a ranar Juma’a 31 ga watan Junairun shekarar 2020, bayan da kishiyar mahaifiyarta ta kai ta wajen zubar da ciki. “Bayan laukar cikin na tsawan watanni takwas, a ranar Juma’a 31 ga watan Junairun shekara 2020, sai kisiyar mahaifiyarmu mai suna Sadiya Sani ta kai ni wani gida a kauyen Sankara domin a zubar da cikin, sau biyu likita yana min allurer zubar da ciki. “A washagarin ranar Asabar 1 ga watan Fabrairun shekarar 2020, na haifi jariri na miji, sannan na kashe shi nan take, inda na dauke shi zuwa daji, sannan na birne shi.”

Jinjiri ya ci gaba da cewa, wacce ake zargin ta kai tawagar ‘yan sanda zuwa wajen da ta birne jaririn, inda aka hako shi aka kai shi zuwa babbar asibitin Ringim kafin a kammala gudanar da bincike. Ya ce, wacce aka zargin ta amsa cewa, ita ta kashe jaririn tare da taimakon kishiyar mahaifiyarta, inda suka birne jaririn a cikin daji. Ya ce, ‘yan sanda sun damke wani matashi mai suna Nasiru Rabiu wanda shi ne ya yi wa budurwar ciki.

Majiyarmu ta ruwaito mana cewa, mahaifiyar yarinyar tare da matashin da ya yi mata cikin suna shirin yi musu aure nan da wata biyu masu zuwa.

Jinjiri ya ci gaba da cewa, an mika lamarin ga sashen rundunar ‘yan sanda masu binciken muyagun laifuka domin gudanar da cikakken bincike.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: