Connect with us

RIGAR 'YANCI

Cibiyar Musulunci A Saudiya Ta Tallafa Wa Marayun Zamfara Da Miliyan N164

Published

on

Cibiyar tallafa wa Musulmi da ke kasar Saudiya, International Islamic Organasation World Muslim League, ta talllafa wa marayun jihar Zamfara da Naira miliyan 164.

Mai ba wa gwamnan Zamfara shawara da wayar da kai da kuma kafafen yada labarai, Malam Zailani Bappa, ne ya bayyana haka a takardar da ya raba wa ‘yan jarida a Gusau, Babban birnin jihar ta Zamfara, inda marayu 600 da a ka tantance 300 ne za su amfana da wannan tallafin kudin a fadin jihar.

Gwamna Bello Muhammad Matawalen Maradun ya jinjina wa wannan kungiyar da ta yi tattaki tun daga kasar Saudiya, domin ta bai wa marayun jihar wannan tallafi, inda ya kuma ce, wannan tallafin ya zo a daidai da lokacin da ya dace, don tun a shekarar 2011 zuwa yau sakamakon ta’addacin mahara ya sanya alkaluman marayu ya karu a wannan jihar.

“Don haka mu ke kara neman dauki daga wasu kungiyoyin, don tallafa wa wadanda mahara su ka maida su marayu,” in ji gwamnan.

A nasa jawabi shugaban kawo tallafin daga Saudiya, Sheikh Ahmad Muhammad Attayyib, ya bayyana jin dadinsa ga yadda gwamnatin Zamfara ta dukufa wajan taimaka wa marayun jihar.

Sheikh Attayyib ya jinjina wa Gwamna Matawalle wajen sadaukar da rabin albashinsa har zuwa karshen mulkinsa ga gidan marayun jihar da kuma yadda ya tsaya tsayin daka wajen ganin marayun sun samu ingantace ilimi da walwala.

Kwamishina Ma’aikata lamuran Addini na Jihar Zamfara, Dakta Tukur Sani Jangebe, ya yi tsokaci a kan rawar da gwamnatin jihar Zamfara ke takawa wajen taimaka wa marayun da marasa galihu har da masu tabin hankali.

A karshe ya mika godiyarsa ga tawagar su Sheikh Ahmad Muhammad Attayyib da su ka kawo ma na wanna tallafi da fatan Allah ya yi mu su sakayya da gidan aljana, sannan ya cigaba da kare gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Matawalen Maradun bisa kudirorinta na alheri.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: