Connect with us

MANYAN LABARAI

Da Dimi-Diminsa: Ka Da Ka Sake Zuwa Borno, Shekau Ga Buhari

Published

on

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya aike wa shugaban kasa Muhammadu Buhari sakon gargadi inda ya gaya masa cewa kar ya kara saka kafar sa zuwa jihar Borno.

 

Shekau wanda ya yi furucin a cikin wani faifan bidiyo, wanda jaridar TheCable ta saki a shafinta, ya nuna yadda shugaban yan tada kayar bayan ya takarkare; gaban sa gadi, ya ce shugaba Buhari ya sani kan cewa yaransa suna nan a kowane lungu da sakon yankin arewa maso gabas.

 

Ya ce, idan ko ba haka ba za su dauki matakin kai wa shugaban kasa hari, muddin ya kara kai wata ziyara a Borno.  “Buhari ka sake zuwa Maiduguri ka gani, ba kana ganin cewa kai daukaka ba. Kar ya kara gwada yin haka nan gaba”. In ji Shekau a cikin bidiyon, wanda ya yi a harshen Hausa.

 

A lokacin da ya koma kan batun sako yan makarantar Chibok, Shekau ya bayar da sharadin cewa babu ta yadda za su saki yan matan matukar gwamnatin tarayya ba ta sako mata mambobinta da take rike dasu ba.

 

Idan dai za a iya tunawa, mayakan sun yi awon gaba da yan makarantar Chibok kimanin 276, a ranar 15 ga watan Apirilun 2014 daga makarantar sakandiren yan mata da ke garin.

 

Wanda tun daga wancan lokacin, maharan Boko Haram din sun sako wasu kadan daga cikin su, tare da ci gaba da rike sauran, ciki kuwa har Leah Sharebu, ta makarantar Dapchi.

 

A hannu guda kuma, maharan sun kai wani farmaki a birnin Maiduguri, yan awanni da kai ziyarar jajantawa jama’ar jihar Borno, da shugaba Buhari ya kai a ranar Laraba, bisa mummunan harin da mayakan suka kai wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 30 a kauyen Auno a Borno.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: