Connect with us

JAKAR MAGORI

Dan Acaba Ya Gurfana A Kotu Bisa Satar Ayaba

Published

on

A ranar Litinin ce, wani dan acaba mai suna Enejo Isah ya gurfana a gaban wata kotu mai daraja ta daya da ke garin Mpape cikin Abuja, bisa tuhumar sa da satar ayaba wanda kudinta ya kai Naira miliyan 1.8. shi dai Isah yana zaune ne a yankin da ake kira Ajegunle cikin garin Mpape, ya na fuskantar tuhumar shiga gidan mutane ba tare da izini ba da kuma laifin sata.

Lauya mai gabatar da kara M.M. Austin, ya bayyana wa kotu cewa, Isah dan shekara 26 da haihuwa, ya fada cikin gidan wani mutum mai suna Emmanuel Tanko ba tare da izini ba, inda ya sace ayaba wanda kudinta ya kai naira miliyan 1.8.

Austin ya bayyana cewa, wanda ake tuhumar ya hada kai ne da wani mai suna Solomon, sannan suka aikata laifin. Ya kara da cewa, Tanko ya kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sandar na garin Mpape. A cewar Austin, wannan laifi ne wanda ya saba wa sashe na 97 da 288 na fanal kot.

Sai dai Isah ya musanta laifin da ake tuhumar sa da shi.

Alkali mai shari’a Salihu Ibrahim, ya bayar da belin wanda ake tuhuma kan kudi na naira miliyan daya tare da mutum daya mai tsaya masa. Ya dage sauraron wannan kara har sai zuwa ranar 13 ga watan Fabrairu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: