Connect with us

RAHOTANNI

Gobara Ta Tashi A Dakin Kwanan Dalibai Na Kwalejin Dayi

Published

on

Gobara ta kona dakunan kwanan dalibai na kwalejin kimiyya da fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Garin Dayi ta karamar hukumar Malumfashi.

Da ya ke yi wa manema labarin bayani, shugaban kwalejin Alhaji Sambo Yaro ya ce gobarar ta fara da misalin karfe 8:00 na daren ranar Lahadi ne a yayin da daliban su ke a azuzuwansu, domin karatun yamma, wato ‘evening prep’.

Alhaji Sambo Yaro ya bayyana cewa, ba a samu rasa rayuku ba, sai dai dukkanin kayayyakin dalibai sun kone kurmus.

Ya bayyana cewa, kwamitin gudanarwar kwalejin zai hada rahoto a kan hadarin gobarar, don mikawa ga gwamnatin jihar ta Katsina da ta tarayya.

Sannan jami’an ’yan sanda da na ’yan sandan ciki da jami’an kashe gobara za su gudanar da bincike a kan masabbabbin afkuwar bala’in gobarar.

Tun dai Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi, Mai shara’a Sadik Abdullahi Mahuta da jami’an karamar hukumar ta Malumfashi karkashin jagorancin Daraktan Sashen Mulki na karamar hukumar Abdulrahman Marafa suka kai ziyarar jaje ga hukumar makarantar.

Sun yi roko ga hukumomin da abin ya shafa da su taimakama kwalejin wajan gina wani dakin kwanan daliban. Wakilin mu na shiyyar Malumfashi ya ruwaito cewa jami’an yan kwana kwana da jama’ar garin Dayi ne suka kashe gobarar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: