Connect with us

LABARAI

Gwamnan Kogi Ya Dakatar Da Shugabannin Manyan Makarantu Biyu

Published

on

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya dakatar da mataimakin shugaban Jami’ar jihar Kogi (KSU) da ke Anyigba, Farfesa Abdulkadir da kuma shugaban kwalejin kimiyya da fasaha na jihar (Kogi Poly), Farfesa Atureta, saboda zargin rashin bin ka’idar tsarin asusun bai-daya (TSA), wanda gwamnatin jihar ta bullo da shi kwanan nan.

Kamar yadda rahoto ya nunar, rashin bin ka’idar bullo da tsarin na TSA da manyan jami’an gwamnatin biyu su ka yi tamkar raina gwamnatin ne.

Kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Mista Kingsley Femi Fanwo, ne ya tabbatar da dakatar da shugabanin manyan makarantun biyu na jihar, sannan ya ce, ko a ranar 7 ga wannan wata na Fabrairu ma Gwamna Yahaya Bello ya dakatar da babban daraktan asibitin kwararru na jihar (Kogi State Specialist Hospital) da ke Lokoja, Dakta Ahmed Attah, wanda shi ma a ke yi wa zargin ya ki bin dokar tsarin na asusun bai-dayan. Sabili da hakan ne ma Mista Fanwo ya bukaci manyan ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar da su gaggauta bin ka’idar sabon tsarin na TSA, inda kuma ya jaddada cewa gwamnati za ta sa kafar wando guda da duk wanda ya saba wa dokar ta TSA a jihar Kogi.

Sai kwamishinan ya ce, Gwamna Yahaya Bello ya bullo da tsarin ne, don amfanin jihar da al’ummarta gabadaya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: