Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamnatin Kogi Za Ta Sauya Wa Mabarata Matsuguni

Published

on

A kokarin da take yi na tsaftace garin Lokoja, babban birnin jihar da kuma sauran manyan manyan garuruwan Jihar, gwamnati jihar Kogi ta bullo da tsarin sauyawa mabarata da kuma gajiyayyu dake barace barace a biranen matsuguni. Kwamishinan kula da harkokin mata da walwalar jama’a na jihar, Hajiya Fatima Kabir Buba ce ta furta hakan a yayin da take yiwa manema labarai jawabi a ofishinta dake Lokoja a jiya laraba. Hajiya Fatima Buba wanda take kokawa game da mabaratan dake barace barace a wurare irinsu dandalin Paparanda da Post Office da kuma shataletalen NTA dake Lokoja,tace gwamnatin Jihar zata wayar musu da kai kafin ta dauki matakan sake tsugunar dasu. Kwamishinan ta kuma ce ma’aikatanta ya samar da kayayakin wayarwa da mabaratan da gajiyayyun kai game da muhimmancin kauracewa wuraren da a yanzu suke zaune don yin bara. Hajiya Fatima Buba kazalika tace mabaratan da kuma gajiyayyun mutane kamar kowa kuma suna da yanci kamar yadda kowaya keda shi,akan haka ta bayyana cewa za a lallashe su don ganin sun kauracewa wuraren da suke barace baracen ba tare da an tilasta musu ba. Kwamishinan ta kara da cewa ma’aikatanta zai hada hannu da ma’aikatan kula da muhalli na Jihar domin magance matsalar wanda a cewarta ke neman gagarar kundila a jihar ta Kogi. Daga bisani Hajiya Fatima Buba ta jinjinawa gwamna Yahaya Bello a bisa kawo gagarumin sauyi cikin Jihar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: