Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Gwamnatin Tarayya Na So Jaridar LEADERSHIP Ta Hana Bayan Gida A Waje

Published

on

Gwanmatin Tarayyar Nijeriya ta nada jaridar LEADERSHIP a matsayin jagorar hadin gwiwar yekuwar yaki da yin bayan gida a fili a dukkan fadin Tarayyar Nijeriya.

Ministan Kula da Albarkatun Ruwan kasar, Injiniya Suleiman Hussaini Adamu, ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyarar aiki a babban ofishin kamfanin LEADERSHIP da ke da mazaunin ta a Abuja a shekaran jiya.

Idan za a tunawa, a shekarar da ta gabata ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu na musamman  mai dauke lamba 009, wato (Edecutive order 009) wadda ke da taken” kawo karshen yin bayan-gari a fili a kasar Nijeriya a shekara ta 2025 da kuma sauran wasu al’amura”.

Sanya hannu ga odar don a tabbatar da kasar Nijeriya ta kawo karshen yin bayan-gari a fili nan da shekara ta 2025.

Haka kuma kimanin mutane Miliyan 47 na kasar Nijeriya, wadda ya kasance kashi 25 na adadin ‘yan kasar ke yin bayan-gari a fili, wanda ya yi sanadiyyar kasar ta zama ta biyu a cikin kasashen duniya da kuma zama ta farko a kasashen nafiyar Afirka da ke yin hakan, wanda kuma ba tsarin kiyon lafiya ba ne ga ‘yan kasar Nijeriya.

Bugu da kari, Ministan ya sanar da nadin kamfanin LEADERSHIP a matsayin jagora na hadin gwaiwar yekuwa ne sakamakon jajircewarsa a harkar.

Ya ci gaba da bayyana gamsuwarsa kan kamfanin LEADERSHIP a jagorantar yekuwar yaki kan yin bayan-gari a fili ga jama’ar kasar nan. Haka zalika kasar ta Nijeriya za ta cimma muradun yekuwar nan da shekara ta 2025 mai zuwa.

Har ilayau ya kara da cewar “akwai bukatar wayar da kan jama’a kan yin bayan-gari a fili da kuma illolin da ke tattare da yin hakan da kuma ilimanta da su kan kiyon lafiyarsu dangane da irin dabi’un jama’ar kasar kan yawan gudanar da bayan-gari a budaddun wurare wanda shi ya nuna cewar babu halaye na tsaftace muhallai ga jama’ar.

Haka zalika ya koka kan wasu ma’aikatun gwamnati kan rashin bayar da goyon baya ga wasu tsare-tsaren da kuma manufofin gwamnati, musamman irin makarantu, ofisoshin gwamnati, kasuwanni da kuma tashoshin mota da sauransu, da kuma yin kalaman banza wurin magance matsalar yin bayan-gari a fili ga mutanen kasar nan.”

Ministan  ya kara da cewar “za mu yi amfani da damar yekuwar fadakarwa kan illolin yin bayan-gari a fili don aika sako kan illolin da ke tattare da yin bayan-gari, wanda wani lokaci jama’a da dama na amfani da kara wurin gogewa bayan sun kammala bayan-gari a fili, wanda ba karamar illa yake haifarwa ba.”

A cewarsa “za mu tabbatar da cewa wurin gudanar da yekuwar, mun samu taimakon ‘yan Majalisar Dokoki na tarayya don yin doka da za ta hana yin bayan-gari a fili, don ta yin haka ne kawai za a iya samar da kyauwan tsaftace muhalli a kasar nan”.

“Haka kuma za mu tabbatar mun samar da fanfunan ruwa a wasu sassa, don shi ne zai bada dama da kuma karfafa wa jama’a da su bude gidajen yin bayan-gari na kasuwa,” in ji Ministan.

Har ila yau, Ministan ya bayyana cewar “yekuwar ta samu nasara domin a shekarar 2017, kasar Nijeriya ta samu nasara ga wata Karamar Hukuma kan cin nasara hana yin bayan-gari a fili, a yanzu ana da kannan Hukumomi 20 a duk fadin kasar da akan bayyan su a matayin Kannan Hukumomin da suka samu nasarar yaki da yin bayan-gari a fili.

Ya kuma bada misali da kasar Indiya, wacce ta kasance ta daya a kasashen duniya kan yin bayan-gari a fili, amma a cikin  shekaru biyar an samun nasarar yakin hana mutanen duniya miliyan 500 yin bayan-gari a fili.

Ministan ya ce, “kamar yadda muka gabatar a cikn jawabi, a kasar Indiya yanzu ta samu nasarar yaki da hana yin bayan-gari a fili dari bisa dari.”

Bisa ga haka ya bayyana cewa rashin wadatar hanyar samar da ruwa wani kalubale ne da ke sa ana samun nakasu ga yekuwar hana yin bayan-garin a fili samun nasara a kasar nan.

A cewarsa, “da kauye da birane na fuskantar karancin samar da ruwa na daya daga cikin  matsalar da ke dakushe yekuwar. Haka kuma gwamnatocin jihohi da kuma masu ruwa da tsaki su ne jagororin nasara ga yekuwar yakin hana yin bayan-gari a fili ga kasar mu Nijeriya.”

Ya ce, “za ka ga gwamnatocin jahohi na gudanar da gine-ginen da jahohin nasu za su zama kamar kasar Dubai ko kuma wasu kasashen Turai, amma sun kasa magance bukatun jama’ar su, musamman samar musu da wadataccen ruwan sha.”

Daga nan sai ya yi kira ga kamfanin LEADERSHIP a cikin shirin yekuwar da su bada goyon baya kan harakokin tsaftace muhalli, wanda aikin ne na jama’a.

Da ya ke maida jawabi, Shugaban kamfanin LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah ya yi godiya ga Ministan kan wannan ziyara da nadin kamfanin nasa da kuma irin kwarin gwiwar da yake da shi ga kamfanin na jagorantar yekuwar.

Saboda haka ya ba shi tabbacin goyon bayansu da na ma’aikantan kamfanin kan jagorantar yekuwar hana yin bayan-gari a fili ga ‘yan kasar Nijeriya don tabbatar da an samu nasarar gudanar da ayyukkan.

Saboda haka nan take Mista Sam ya bada umurni ga dukkan shugabannin sashe na kamfanin da su tabbatar da cewa sun dauki wannan aikin a matsayin wani aiki na musamman da za su gudanar don samun nasara, wanda zai zama daya daga cikin ayyukkan da suka rataya ga kamfanin zai sauke da kuma sauran al’ummar na kasar nan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: