Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnatin Tarayya Ta Zabi Ganduje Zakara A Fannin Harkar Lafiya

Published

on

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karrama Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bisa kokarinsa na cigaban harkokin lafiya a matakin farko a jiharsa ta Kano, wanda ya samar da kyawawan manufofi irin wanda duniya ke kai yanzu. Kazalika, Shekaru 27 kenan da a ka taba bai wa wani irin wannan lambar karramawa a bangaren harkokin lafiya.

Kafin baiwa Gwamna Ganduje wannan Lambar Karramawa, wanda Ministan harkokin lafiya, Dakta Osagie Emmanuel Enahire, Babban Darakta Harkokin Lafiya a matakin farko na kasa (NPHCDA), Dakta Faisal Shu’aib ya bayyana cewa, “a baya lokacin da aka taba bayar da irin wannan Lambar Karramawa, yanzu haka ya kwashe kusan shekaru 27 da suka wuce. Yanzu kuma, ga shi muna karrama Gwamna Ganduje da wannan Lamba ta yabo, na kasancewa Zakara a harkokin kiwon lafiya.”

Haka zalika, an bayar da wannan Lamba ta karramawa a taron tattaunawa kan harkokin lafiya na shekara ta 2020, wanda aka gudanar a babban dakin taro na Coronation da ke Fadar Gwamnatin Jihar Kano, ranar Talatar da ta gabata.

Da ya ke gabatar da nasa jawabin, a lokacin bayar da Lambar Karramawar, Dakta Shu’aibu ya bayyana cewa, “mun yi la’akari da kyakkyawan jagorancin da ya haifar da kuma nasarar da aka samu a tsarin ayyukan lafiya, sakamakon ingantaccen kasafin kudi da ake warewa bangaren da kuma kyakkyawan jagoranci kafin kammala tantance, wanda ya samu nasarar lashe wannan gagarumar karramawa.”

Ya kara da cewa, kyakkyawan jagorancin da Gwamnan ke aiwatarwa, a kokarinsa na ciyar da harkokin lafiya a matakin farko a Jihar Kano, wanda ya yi sanadiyyar sauran jihohin ke kwaikwaya daga Jihar Kano, wannan shi ma wani dalili ne da ya sa Gwamna Ganduje samun wannan nasara a bangaren harkokin lafiyar.

Da ya ke bayyana gamsuwarsa tare da kuma ta Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, a lokacin gabatar da Lambar Karramawar ga Gwamna Ganduje, Ministan ya ce matsayin da Kano ke tafiya akansa ta fuskar ci-gaban harkokin lafiya a matakin farko, ko shakka babu abin karfafa guiwa ne kwarai da gaske.

Har ila yau, da yake bayyana yadda Gwamna Ganduje ya kai ga zama Zakara a wannan bangare na harkokin lafiya a kasa baki-daya, Minista Enahire ya bayyana cewa, “mu a Ma’akatar Lafiya ta kasa, mun hadu wajen yanke hukuncin da ya kai ga baiwa Gwamnan wannan Lambar Karramawa.”

Ya cigaba da cewa, dukkanin alkaluman da aka gindaya kafin zuwa wannan mataki, a hakikanin gaskiya sun bayyana gamsuwarsu da gagaruman gudunmawar da Gwamna ke bayarwa a bangaren da aka ambata a tsarin harkokin lafiya a matakin farko.

Da ya ke bude taron tattaunawar, Minstan harkokin lafiya na tarayya ya bayyana cewa sakamakon gamsuwa da yarda da kokarin da Gwamna Ganduje ke yi a bangaren harkar lafiya baki daya, Jihar Kano na yin bakin kokari a wannan sashi. Domin ba zai yiwu ace nazo kawai ba tare da gamsuwa da abubuwan da Gwamna ke aiwatarwa kyawawa ba.”

Sa’annan, Enahire ya bukaci Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Ganduje, ta fahimci amfanin bangaren lafiya ba kuma tare da yin wasarairai da sauran bangarorin Jihar Kano ba. Sakamakon bibiyar aikace-aikace tare da gane wa idanummu. Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Gwamna ne wanda ya himmatu wajen inganta harkokin lafiya ga al’ummar Jihar Kano, wanda kuma ke yin aiki domin inganta harkokin lafiya.”

Da yake ci-gaba da gabatar da nasa jawabin, Babban Daraktan NPHCDA, Dakta Shu’aib, ya tuna yadda Jihar Kano karkashin Gwamna Ganduje ta yaki cutar Polio har sai da ya kai ta kasa,” tun lokacin da Ganduje na matsayin mataimakin Gwamna. Jihar Kano da kasa baki-daya, ba za su manta da kokarinka ba a wannan bangare,” in ji shi.

Lokacin da mai girma Gwamna ya bujiro da kyakkyawan tunani a kan muhimmancin kiwon lafiya, ta yadda ya bujiro da ingantattun matakai wajen shirye-shiryen inganta harkokin lafiya, a bayyane yake Jihar Kano ta samu albarka a kan haka. Kowa ya san haka, cewar Gwamna na yin abubuwan da ake alfahari da su a wannan bangare.”

A cewarsa, shigar mata cikin harkar lafiya, wata hanya ce da ta taimakawa harkokin lafiya a matakin farko, wadda ta zama mai karsashi tare da samun goyon baya tun daga matakin farko, inda ake fatan samun kyakkyawar makoma.

Da ya ke gabatar da nasa jawabin, Gwamna Ganduje cewa ya yi, taron tattaunawar wani harsashi ne a bangaren lafiya, musamman lafiya a matakin farko a Jihar Kano.

“Dukkaninmu mun aminta da cewa jin dadin al’umma daga kasa wani gimshiki ne da ya kamata a yi la’akari da shi.”

Ya kara da cewa, Jihar Kano na zuba dukiya mai tarin yawa domin samun nasarar ayyukan Hukumar Lafiya a matakin farko a Jihar Kano.

Jim kadan bayan bude taron tattaunawar, an raka Minisatan zuwa Cibiyar lura da cutar Kansa, wadda ake aikinta a halin yanzu, wadda Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya kaddamar da sanya harsashin gininta a makwannin da su ka gabata tare da duba aikin Cibiyar.

Kafin ziyarar duba aikin, sai da ya yi jawabi ga wasu mata wadanda suka haura su 500, aka kuma gana da su a kusa da Asibitin Muhammadu Buhari, ‘yan mitoci kadan kafin isa Cibiyar Lura da Cutar ta Kansa, inda aka duba su kyauta, domin kaddamar da shirin ranar yaki da Cutar Kansa na duniya ta shekarar 2020.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: