Connect with us

LABARAI

Harin Auno: Shure-shuren Mutuwa Boko Haram Ke Yi – Buhari

Published

on

  • Matasan Maiduguri Sun Fara Fusata

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayar da tabbacin cewa, hare-haren da ’yan kungiyar masu tayar da kayar baya na Boko Haram ke zafafa kai wa a baya-bayan nan alama ce ta shure-shuren mutuwa, wanda hakan ba zai hana kawo karshensu a Nijeriya ba.

Shugaba Buhari ya yi wannan ikirari ne a lokacin da ya ke mika jajensa ga gwamnatin Jihar Borno, kan sababbin hare-haren da a ke samu a fadin jihar, musamman a kauyen auno da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, don nuna alhini ga al’ummar jihar game da mummunan harin na ta’addanci, wanda mayakan Boko Haram su ka kai a kauyen na Auno,

Don haka sai shugaban ya yi gargadin cewa, ”sake dawo da kai hare-haren da wadannan ’yan ta’adda, ya nuna yadda su ke jan numfashinsu na karshe a duniya.”

Ya kara da cewa, “ko shakka babu, sojojinmu a shirye su ke tare da cigaba da samun sabbin kayan yaki na zamani da nuna kwarewa a fagen fama a fafatawarsu da sauran gyauron mayakan Boko Haram, kuma a kowane lokaci za su yi biji-biji da su.

”Sannan kuma duk da wannan kalubalen da a ke fuskanta a baya-bayan nan, idan a na batun sabon salon yakin sunkuru, duk da sojojinmu ba su da masu tamaka mu su, amma su na da karfin da za su turmushe wadannan makiyan al’umma.”

To, sai dai kuma kafin gabatar da wadannan bayanan nasa, Shugaban Kasar ya fuskanci fushin wasu hasalallun matasa a kan hanyarsa ta zuwa gidan gwamnatin jihar bayan ya sauka a filin jiragen sama da ke Maidugurin, inda su ka rika yi wa tawagarsa ihu, su na cewa “ba ma so! Ba ma yi!”

An ruwaito al’ummar garin, wadanda su ka yi dafifi a gefen hanyar da ta fito daga filin jiragen saman Maiduguri, fuskokinsu cike da alamar rashin gamsuwar dangane da yadda Gwamnatin Tarayya ke fuskantar matsalolin tsaron da ke cigaba da addabar yankin.

Shugaban Kasa Buhari, wanda ya yada zango a birnin Maiduguri daga babban Addis Ababa, birnin Ethiopia, wato kasar Habasha, domin kai ziyarar jajenta wa jama’ar jihar hadi da gwamnatin jihar Borno, bai taba fuskantar makamancin irin hakan ba a yankin Arewa maso Gabas, wanda ke fama da matsalar tsaro tun kafin ya hau karagar mulki a zangonsa na farko cikin shekarar 2015.

Idan dai ba a manta ba, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bar birnin Abuja tun ranar Jumu’ar da ta gabata zuwa halartar babban taron Kungiyar Kasashen Afrika (AU) Karo na 33 a birnin na Addis Ababa.

A cikin wata sanarwar da mai taimaka wa Shugaba Buhari kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya fitar ya ce, Fadar Shugaban Kasar ta nuna alhininta tare da jaje ga iyalan da wannan ibtila’in ya shafa a jihar.

Ya ce, gwamnatin Buhari za ta cigaba da kokarin yakar matsalar Boko Haram har sai abinda hali ya yi tare da shan alwashin dakile yunkurinsu wajen kama wani yankin Nijeriya.

Daga dukkan alamu, Shugaba Buhari ya je Maidugurin ne, domin cika wannan alkawari. Don haka ya zarce can din kai-tsaye wajen taron, don ziyarar gani da ido.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: