Connect with us

WASANNI

Ighalo Zai Buga Wasanmu Da Chelsea, Cewar Solkjaer

Published

on

Tsohon dan wasan tawagar Super Eagles ta Nigeriya, Odion Ighalo yana cikin ‘yan wasan da za su fuskanci kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a gasar firimiya ranar Litinin kamar yadda kociyan Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya tabbatar.

Ighalo bai je wasannin atisaye da kungiyar ta yi a Spaniya ba, sakamakon tsoron yada cutar coronabirus dalilin da aka hana shi takardar izinin shiga kasar kuma ya zauna a kasar Ingila domin ci gaba da daukar horo.

Dan kwallon tawagar Najeriya, mai shekara 30 ya koma Manchester United da buga wasan aro daga kungiyar kwallon kafa ta Shanghai Shenhua a ranar 31 ga watan Janairu, wato ranar da aka rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa a nahiyar turai.

Tsohon dan kwallon Watford din ya koma buga gasar China a shekarar 2017, inda ya fara da kungiyar Changchun Yatai sai dai bayan da ya buga kakar wasa biyu sai ya koma Shanghai Shenhua wadda ya buga wa wasanni 19 ya kuma ci kwallo 10.

Ighalo ya taka rawar gani a gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a Masar, inda ya ci kwallo biyar wadda hakan tasa ya lashe kyautar wanda yafi zura kwallo a gasar, kuma ya zura guda bakwai a wasannin neman gurbin shiga gasar

Rabon da Ighalo ya buga kwallo tun ranar 6 ga watan Disamba a lokacin da ya canji dan wasa a karawar da Shanghai Shenhua ta doke Shandong Luneng 3-0 a gasar FA Cup ta China sai dai a ranar Litinin zai fuskan Chelsea

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: