Connect with us

RIGAR 'YANCI

INEC Ta Fitar Da Jadawalin Zaben Cike Gurbin Majalisar Wakilai A Neja

Published

on

Hukumar zabe ta kasa, INEC, ta fitar da jadawalin zaben cike gurbi na kujerar dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rijau da Magama a jihar Neja.

Tunda farko da yake bayani kan jadawalin, shugaban hukumar zabe ta kasa, reshen jihar Neja. Farfesa Sam Egwu yace hukumar ta amince da sanar da al’umma wannan zaben wanda sashe 30 sakin layi na 3 a dokokin zabe na shekarar 2010.

Farfesa Egwu ya ce, hukumar ta tsayar da zaben fidda gwani na ‘yan takarar jam’iyyun siyasa, da zai gudana daga 10 zuwa 16 ga watan Fabrairun da muke ciki akan sashin na 87 na kundin tsarin zaben kasar nan na shekarar 2010.

Hukumar tace ranar 18 ga watan Fabrairun jam’iyyun siyasa zasu gabatar da takardun ‘yan takarkarun da wadanda aka zabo bisa sashin dokokin zabe sashi na 31 na dokar zabe ta 2010.

Egwu yace hukumar ta tsayar da ranar 25 ga wannan watan a matsayin ranar karshe na kai sunayen ‘yan takara, bisa saahi na 31 sakin layi na uku.

Ranar 29 ga watan nan dai, itace jam’iyyun siyasar zasu gabatar da sunayen jami’an sanya ido da masu kula da zaben ga hukumar zaben.

Farfesa Sam Egwu ya jawo hankalin jam’iyyun siyasa da su bi dokokin zabe wajen bai wa hukumar zaben damar sanya ido akan yadda zasu gudanar da zaben fidda gwani kamar yadda dokar zabe ya tsara. Yace hanya biyu ce ake gudanar da zaben fidda gwani, akwai hanyar ‘yar tike ko kuma kada kuri’a koda jam’iyya dan takara tilo ta ke da shi.

Hukumar ta bayyana cewar masu kada kuri’a a kananan hukumomin Magama da Rijau sun kai jimillar 159,347 a mazabu 309 a yankuna 24 na dukkanin kananan hukumomin.

Karamar hukumar Rijau mai nisan zango daga Minna fadar gwamnatin jihar kilomita 330, yayin da karamar hukumar Magama tana da nisan kilomita 320 daga minna fadar gwamnatin jiha. Karamar hukumar Rijau tana da mazabu guda 13 yayin da Magana na da mazabu 11.

Shugaban ya bayyana cewar hukumar ta tsayar da ranar 12 ga Maris a matsayin ranar da za a tsayar da yakin zaben ‘yan takarkarun da jam’iyyun siyasar su ka zabo dan yi masu takarar. Yayin da ranar 14 ga watan Maris din zai zama ranar zaben cike gurbin bisa sashe na 116 sakin layi 1 na dokokin zaben 1999 wanda aka yiwa gyaran fuska a shekarar 2010 sashe na 25 sakin layi 3.

Shugaban hukumar ya ce, ya na fatar wannan zaben cike gurbi jama’a za su fito dan zaben wanda suke ra’ayi, duba da rashin fitowar jama’a a zaben da hukumar zaben jiha ta gudanar a karamar hukumar Agwara a makonni baya.

Alhaji Yahaya Ability mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a yankin Neja ta arewa ya jawo hankalin hukumar zabe ta kasa, da ta tabbatar tayi anfani da jami’an kula da yaki da rashawa kamar hukumar zaben jihar ta yi a zaben dan majalisar jihar da a ka gudanar a karamar hukumar Agwara.

Ability ya yaba wa jami’an tsaro kan yadda suka gudanar da aiki a wannan zaben da ya gabata, ya neme su a wannan karon ma su sake bada gudunmawa wajen ganin an gudanar da zabukan ba tare da hargitsi ko tashin hankali ba.

Taron dai an gudanar da shi ranar Litinin din makon nan a dakin taro na hukumar zaben ta kasa da ke Minna.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: