Connect with us

RIGAR 'YANCI

Kasar Hungary Za Ta Taimaka Wa Jihar Nasarawa Kan Harkar Noma

Published

on

Ambasadan kasar Hungary a Najeriya, Dakta Sandor Beer, ya bayyana cewa kasarsa za ta taimaka wa Jihar Nasarawa, daon bunkasa harkar Noma da kuma harkar Gas ta yadda za’a bunkasa tattalin arziki da samar da aikin yi a jihar Nasarawar.

Ambasadan  Dakta Sandor Beer ya ce, yanzu kowa ya san yadda duniya ta karkara a kan harkan noma kuma ya lura jihar Nasarawa tana daya daga cikin jerin jihohin da a Nijeriya a ke jinjina ma ta kan harkan noma.

Saboda haka kasar tasa za ta taimaka wa jihar ta hanyoyin da za ta kara bunkasa da harkar noma.

Akwai kayayakin noma na zamani da irin da takin zamani da sauransu, wanda idan jihar ta samu wannan tallafin zai zarce tsararta ta hanyoyi daban-daban kan harkar noma.

Da yake mai da martani Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya yaba da wannan kokari na Kasar Hungary domin taimakawa jihar Nasarawa.

Gwamnan ya ce; wanan abin farin ciki ne da zai kasance jihar zata hada harka tsakanin ta da wata kasa da za ta samu taimako masamman a harkan noma.

Gwamnan wanda mai taimaka masa ta masamman kan harkokin Gwamnati na birnin tarayya Abuja Yusuf Maiunguwa yace; Gwamnatin jihar Nasarawa karkashin Jagorancin Injiniya Abdullahi Sule tayi murna da jin dadi da wanan abin farin ciki.

Kuma jihar zata rika gudanar da ayyukan ta kafada da kafada tsakanin ta da kasar Hungary. Ya ce; Gwamnatin Nasarawa ta na kokari wajen bunkasa harkan noma kuma manomar jihar su na amfana da takin zamani kan farashi mai sauki.

Ya ce; Gwamnati ta tabbatar da irin nasarorin da take samu a harkan noma saboda ana samun kudaden shiga, kuma alumman jihar Nasarawa suna amfana so sai ta harkan noma.

Jihar na noma abubuwa masu yawa wanda ake fita dasu zuwa wasu jihohin daga yankin Arewa zuwa kudancin Nijeriya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: