Connect with us

WASANNI

Klinsmann Ya Ajiye Aikin Koyar Da Hertha Berlin

Published

on

Mai koyarwa, Jurgen Klinsman, ya ajiye aikin horar da kungiyar kwallon kafa ta Hertha Berlin kuma kamar yadda ya bayyana zai ci gaba da aikin jami’in sa ido a harkokin wasannin kungiyar wanda yabari a baya.

Klinsman tsohon dan wasan Bayern Munich da tawagar kwallon kafar Jamus, ya karbi aikin kociyan kungiyar Hertha Berlin ne acikin watan Nuwamba, bayan da aka kori Ante Cobic, saboda rashin samun nasara.

Tsohon kociyan tawagar kwallon Amurka, mai shekara 55 ya ja ragamar wasanni 10 a Hertha, inda ya ci karawa uku da rashin nasara a wasa hudu kuma yayi canjaras a ragowar wasanni ukun da kungiyar tayi.

A lokacin da ya karbi aikin kungiyar tana kasan teburi da maki iri daya da na Fortuna Düsseldorf, yanzu ta bar gurbin da tazarar maki shida wanda hakan ya nuna cewa yayi kokari a iya dan zamansa a kungiyar.

A farkon watan Nuwamba aka nada Klinsman a cikin mahukuntan Hertha, daga baya aka ba shi aikin jan ragamar kungiyar sai dai shima yanzu ya tabbatar da cewa ba zai iya cigaba da aikin koyar da tawagar ba.

Hertha Berlin za ta buga wasanta na gaba a gasar Bundesliga ta kasar Jamus ranar Asabar a gidan Paderborn, kuma Aledander Nouri ne zai yi aikin rikon kwaryar koyar da ‘yan wasa kafin a samu mai koyarwa na din-din-din.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: