Connect with us

LABARAI

Kotu A Kaduna Ta Daure Matashi Wata 21 A Kurkuku Bisa Yunkurin Sata

Published

on

Kotu Majistare dake zaune a garin Kafanchan ta aika wani matashi mai suna Tobias Solomon zuwa gidan gyaran hali na wata 21 bisa yunkurin da ya yi na yin sata.

 

Solomon an gurfanar da shi gaban kotun ana zarginsa da aikata laifin shiga muhallin da ba na shi ba yana kokarin sata, laifin da aka ce ya sabawa sashe na 333, 313 da 57 na dokar Fenal Kod.

 

Dan sanda mai shigar da kara, Insp. Esther Bishen, ya shaidawa kotun cewa, wani mai suna Akuna Emmanuel ne ya shigar da rahoto gaban ofishin ‘yan sandan dake Kafanchan a ranar 3 ga watan Fabarairu.

 

Bishen ya ce wanda ya shigar da korafi gare su ya yi zargin cewa wanda ake zargi ya shiga gidansa inda ya yi yunkurin yi masa satar wadansu kayayyaki inda shi kuma ya kama shi.

 

Sai dai da aka karantawa wanda ake zargi laifin na sa, ya amsa laifin, inda ya roki kotun da ta sassauta masa a hukunci.

 

Wannan ya sanya mai shigar da kara, ya nemi kotun da ta hukunta wanda ake zargi bisa dokar sashe na 125 (8) na dokar masu aikata laifuka ta jihar Kaduna.

 

Mai shari’a, Mary Adams, ta aika da wanda ake zargi zuwa kurkuku na wata uku ko kuma tarar naira dubu 15 bisa samunsa da shiga gidan, tare da kwashe wata shida a kurkuku ko tarar dubu 15 bisa samunsa da laifin yaudara, da kuma shafe shekara guda a kurkuku ko tarar naira dubu 10 bisa samunsa da laifin yunkurin sata.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: