Connect with us

LABARAI

Ku Bi Gwamnatin Bauchi Ido-rufe – Ladan Ga Ma’aikatan Gidan Gwamnati

Published

on

Sabon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Bauchi, Dakta Ladan Salihu, ya nemi dukkanin ma’aikatan gidan gwamnatin jihar da su himmatu wurin biyayya ga dukkanin umarnin da gwamnatin jihar ta ba su, domin aiki ya rika tafiya bisa daidai kuma cikin inganci.

Ladan ya bayyana hakan ne a wajen bude taron kwakkwafa tunanin ma’aikatan kan harkokin da su ka shafi tsaro da ilmantar da su a kai, domin muhimmancin da hakan ke da shi kamar yadda gwamnatin ta lura.

Dakta Ladan ya ce, daga yanzu ofishinsa zai tsaurara matakan da za su tabbatar ko wane ma’aikacin na tafiyar da ayyukansa yadda gwamnatin ta umurceshi ba tare da kauce wa ka’idodi da dokokin tafiyar da aiki ba.

“Wannan darasin da a ke ba ku na da gayar muhimmanci a gare ku mahalarta, domin karin sani kan yadda za ku tsare dukkanin kayyakin gwamnati da ke hannunku, sannan kuma hakan zai ilmantar da ku wurin tabbatar da kun yi biyayya wa dukkanin umurnin gwamnati wajen tafiyar da aiyukanku.

“Ina cike da farin ciki bisa yadda na ga dukkanin masu jawaban nan su na da kwarewa kan hidimar tsaro wadanda za su ba ku dabaru da hikimomin da za su tabbatar da kai aiki na tafiya salum-alum,” a cewarshi.

Daga bisani sai shugaban ma’aikatan ya nemi mahalarta taron da su nutsu su saurari dukkanin darussan da a ke son su dauka domin tabbatar da aiki na ingantuwa da tafiya bisa yadda a ke nema.

Shugaban Sashen Tsaron Gidan Gwamnatin ta Bauchi (CSO), Bilyaminu Bako, ya shaida cewar hidimar tsaro na da matukar muhimmanci ga kowane ma’aikacin gidan gwamnatin, ya na mai cewar, akwai gayar muhimmancin kowane ma’aikaci ya rungumi hidimar tsaro a kashin kansa domin alfanun da hakan ke da shi, ya na mai cewa, sabbin hikimomin kariya da tsaftace cikin gidan gwamnatin da su ka bijiro da shi a halin yanzu sun yi ne domin komai ya ke tafiya bisa saiti ba wai don su muzguna ma kowani ma’aikaci ba, sai ya nemi ma’aikatan da su ba su hadin kai wajen kyautata tsaron gidan.

Babban mai bai wa gwamnan jihar kariya, ya kuma kara da cewa, jami’an tsaro da hidimar tsaro na da matukar muhimmanci a kula da su, sai ya nemi hadin kan ma’aikata da jami’an tsaron gidan da su kyautata dangantakarsu domin kyautata aiki a kowani lokaci.

Kan rike sirri da amanar tsaro kuwa, Chief Detail na Gwamnan Jihar, Mr B.F Mathias, ya fadi cewar akwai matukar bukagar kowani ma’aikacin da ke gidan gwamnatin ya himmatu gurin rike sirrin gidan, ya na mai fadin cewar, fitar da sirrin gidan gwamnatin barazana ce ga tsaron gidan don haka ya nemi su kiyaye.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: