Connect with us

LABARAI

Ku Daina Damun Mu- Sakon Wadanda Aka Kashe Wa Iyaye Ga Kafafen Watsa Labarai

Published

on

 

Iyalan Marigayi Clement da Toyin Okhide wadanda aka kashe a yankin Ejigbo a jihar Legas a ranar Talata sun nemi kafafen watsa labarai da su daina damun su tare da yada bayanan da ba haka suke ba har su kammala jimamin rashin ‘yan’uwansu.

 

Rahotanni sun tabbatar da cewa iyalan Okhide sun fada cikin jimami ne bayan da ake zargin Michael dan shekara 23 ya kashe iyayensa ta hanyar soka musu wuka.

 

Sai dai a bayanan da iyalan suka fitar a ranar Talata, ya nuna cewa iyalan sun nemi kafafen watsa labarai da su daina kanbama abin tare da yada bayanan da bah aka suke ba.

 

Sanarwar iyalan wanda iyalan Marigayi Dr Abiola Odeyinka, da Miss Ayooluwa Okhide da Master Stephen Okhide suka sanya wa hannu, sun bayyana lamarin da ya faru har iyayensu suka rasa ransu a matsayin abin bakin ciki ga iyalan na su.

Inda suka nemi al’umma da su taya su jaje da alihini musamman a irin wannan lokacin, inda suka ce tabbas illar shaye-shaye da tabin kwakwalwa abu ne da ya kamata a hadu wajen magance shi.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: