Connect with us

JAKAR MAGORI

Magidanci Ya Shiga Hannu Bisa Yunkurin Kashe Matarsa

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Legas ta cafke wani magidanci mai suna Christopher Lament dan shekara 45 da haihuwa, bisa laifin yunkurin kashe matarsa. Lamarin ya faru ne a ranar 2 ga watan Fabrairu a gida mai lamba 23 da ke kan titin Jossy Castro ta Jihar Legas. An bayyana cewa, wanda ake zargi ya yi yunkurin kashe matarsa da wuka lokacin da suka sami rashin jituwa. Ma’auratan sun samu rashin jituwa mai tsanani, bisa yadda magidancin ya kasa daukar nauyin iyalansa bayan ya rasa aikinsa na banki na tsawon shekaru biyar.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, ko dai magidancin ko kuma matar wani na aiki, amma rashin kudaden ciyarwa ya sa magidancin yake kokarin farmakan matarsa saboda ta matsa masa.

‘Yan sanda sun bayyana cewa, sun samu nasarar ceto matar bayan da makwabta suka kai rahoto, sannan sun sami nasarar kwato wukar daga hannun wanda ake zargi.

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, Bala Elkana ya bayyana cewa, ma’auratan sun shafe shekara 13 da yin aurensu, inda a yanzu haka suke da yara biyu. “Dukkan su ‘yan asalin Jihar Akwa Ibom ne. wanda ake zargin ya rasa aikinsa na banki tun shekara biyar da suka gabata, inda a yanzu haka matar ce kadai ke yin aiki. Ma’auratan suna yawan yin fada a tsakanin su sakamakon rashin kudi da kuma karancin kulawa. “Wannan ne ya sa wanda ake zargin ya yi yunkurin soke matarsa da wuka lokacin da suka sami rashin jituwa. A yanzu haka a na gudanar da bincike, indan an kammala za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kuliya,” in ji shi.

Elkana ya ci gaba da cewa, rundunarsa ta samu nasarar damke wani matashi mai suna Isiaka Olalekan, bisa zargin sa da fasa shagon jama’a a ranar 6 ga watan Fabrairu. Ya kara da cewa, wanda ake zargin mai shekaru 19, an kama shi da karamar bindiga a kan gadar Third Mainland Bridge da misalin karfe 7:15 na safe, bayan ya fasa shago mai lamba 287 a kasuwar Boboreji da ke garin Island cikin Jihar Legas, mallakar wani mutum mai suna Faruk Nobi. “’Yan sandan da suke sintiri a kan gadar Third Mainland Bridge suka sami nasarar kama shi. An kwato wayoyin salula masu tsada da kuma karfe balle shaguna daga hannun wanda ake zargi. “Wanda ake zargi dai shi sabon ma’aikaci ne a wajen mai gidansa, ya amince ya sace wannan wayoyin ne daga shagon mai gidansa. Za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kuliya idan aka kammala bincike. “Kwanishinan ‘yan sanda ne ya bayar da umurnin baza tawagar ‘yan sanda a kan gadar Third Mainland Bridge domin dakile fashi a cikin cinkoson ababan hawa,” in ji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: