Connect with us

JAKAR MAGORI

Mai Babur Ya Gurfana Gaban Kotu Bisa Kashe Dan Shekaru 70

Published

on

A jiya ce, rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta gurfanar da wani mutum mai suna Samuel Subair dan shekara 48 da haihuwa, bisa tuhumar sa da laifin kashe wani dattijo mai shekaru 70 babur dinsa. An dai gurfanar da Subair ne a gaban kotun Legas wacce take zaune a gari Ikeja, bisa tukin ganganci a kan babu wanda ya janyo hatsari sannan ya yi sanadiyyar kashe wannan dattijon.

Lauya ‘yan sanda mai gabatar da kara, Sajan Unah Mike, ya bayyana wa kotu cewa, wanda ake tuhuma ya aikata wannan laifin ne a ranar 23 ga watan Junairun shekarar 2020 da misalin karfe 10.05 na dare a yankin Iyana Ipaja kanb babban titin Legas zuwa Abeokuta, lokacin da yake kan babur dinsa kirar TVS mai lamba kamar haka AGL 468 QH.

Sai dai Subair ya musanta laifuka guda biyun da ake tuhumar sa da shi.

Alkali mai shari’a Mista A. A. Fashola, ya bayar da belin wanda ake tuhuma a kan kudi na naira 250,000 tare da mutum daya mai tsaya masa, sannan ya dage sauraron wannan kara har sai ranar 24 ga watan Fabrairun shekarar 2020.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: