Connect with us

JAKAR MAGORI

Mai Sayar Da Magani Ya Lakada Wa Jigon APC Duka Har Lahira

Published

on

An samu tashin hankali a garin Owerri da ke babbar birnin Jihar Imo, a ranar Asabar lokacin da wani mai sayar da magunguna tare da ma’aikacinsa suka lakada wa wani jigon jam’iyyar APC mai suna Damian Ali, duka har lahira.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, lamarin ya faru ne a mahadar hanya ta

Umuguma da ke yankin World Bank cikin garin Owerri. Jami’an ‘yan sanda daga garin Owerri ne suka samu nasarar shawo kan wannan tarzoma daga yankin. Majiyarmu ta kara da cewa, mamacin dan asalin garin Nkarahu da ke cikin karamar hukumar Ohaji/Egbema ta Jihar Imo, shi dai babban jigo ne a jam’iyyar APC kafin ya mutu.

Magajin mamacin mai suna Mista Dominic Okpor, ya bayyana wa manema labarai a ranar Lahadi cewa, mai sayar da magunguna tare da ma’aikacinsa sun lakada wa Ali dukan kawo wuka har sai da ya mutu, lokacin da mamacin yake kokarin ijiye motarsa a kusa da harabar wajen kasuwancinsu. Okpor ya ce, “sun dai lakada masa duka ne a mahadar hanya ta Umuguma a ranar Asabar, lokacin da mai shagon tare da ma’aikacinsa suka yi kokarin hada mamacin ijiye motarsa a wajen kasuwancinsu.”

Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda jihar, Orlando Ikeokwu, ya bayyana cewa, a halin yanzu mai sayar da magungunan yana hannun ‘yan sanda. Ikeokwu ya kara da cewa, wanda ake zargin shi ne ya kai rahoton kansa wajen ‘yan sanda. Ya ci gaba da cewa, kwamishinan ‘yan sandar jihar, Olaniyi Fafowora, ya bayar da umurnin a gaggauta binciken lamarin. Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar ya ce, “mai sayar da maganin yana hannun ‘yan sanda. Shi ne ya kai rahoton kansa a ofishin ‘yan sanda. Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin a mika lamarin gas ashen rundunar ‘yan sanda masu binciken laifukan kisan kai domin gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kuliya.”

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: