Connect with us

NOMA

Manoman Auduga A Nijeriya Na Fuskantar Kalubalen Masu Saye – Manomi

Published

on

Manoman Auduga a Nijeriya suna fuskantar kalubalen masu sayen Audugar da manoman kasar nan suka noma.

Furucin hakan ya fito ne daga bakin wani babban manomin Auduga Alhaji Abbas Umar Nabingi.

Alhaji Abbas Umar Nabingi wanda ya sanar a hakan a hirarsa da manema labatai a jihar Gombe ya ce, babbar matsalar ita ce idan aka noma wane ne zai saya Idan za a saya kuma za a saye ta ce da karamin farashi ganin tana dawainiyya da yawa.

A cewar manomin na Audugar, gidan su sunyi gadon noman ta ne fiye da shekara 40 kuma har yanzu ba su bar shi ba; inda shi yake noma kadada 50 na auduga.

Alhaji Abbas Nabingi, ya ce a shekarun baya a gidansu baya ga noman auduga suna gurza ta amma yanzu noman auduga a Nijeriya ya mutu kuma gwamnati ba ta shirya farfado da harkar ba.

Alhaji Nabingi, ya ce bayan ba ta da farashi a Gombe babu irin angurya mai kya domin irin da ake nomawa shekara da shekaru har yanzu shi ne idan manomi ya noma faduwa yake yi saboda rashin ingancinsa.

A cewarsa, ya kamata a ce yanzu an samu angurya mai inganci irin wadda ake nomawa a kasar China da sauran kasashen duniya, unda ya kara da cewa, amma ba mu samu wannan ci gaba ba tukuna.

Ya ce, hatta kaji da a ke kiwatawa akwai ’yan watanni haka dabbobi, a masara ma akwai iri mai inganci, inda ya yi nuni da cewa, amma a auduga an bar su a baya.

Ya kara da cewa, a bara sun samu wanda ya kawo musu iri mai kyau kadan suka gwada kuma suka samu alherinsa, inda ya yi kira ga gwamnati ta kawo musu iri mai inganci idan da gaske ta na so ta taimaki manoman auduga.

A cewarsa, abin da ya kara kashe darajar noman auduga a Gombe shi ne rashin tsaro wanda kafin ta gama fasuwa ta nuna makiyaya sun shiga sun cinye audugar, inda ya kara da cewa, a garin Daben Fulani akwai wani manomi da ya zo ya koka cewa yanzu haka makiyaya sun cinye ma sa auduga.

Ya cigaba da cewa, da za a taimaka wa manoman yadda ya kamata su kadai a iya gidansu kawai za su noma kadada dubu uku a garinsu na Dasa Hayin Maido kuma a yankin karamar hukumar Balanga za su iya noma kadada dubu 30, inda ya yi nuni da cewa, mutuwar masakun Nijeriya ta taimaka wajen kara jefa noman auduga cikin halin kunci a Nijeriya.

Ya sanar da cewa, daga shekara 20 zuwa yanzu idan aka noma auduga a kasar nan, kasar Indiya ne su ke zuwa suke saye ta su tafi da ita kuma sai yadda su ka ga dama su ke saye.

Ya bayyana cewa, hanya daya mafita ga noman auduga gwamnati ta tsaya sosai wajen bin hanyoyin da suka dace domin taimaka wa manoma a ga an bunkasa noman auduga a Nijeriya.

A karshe, manomin ya kuma sanar da cewa, ya kamata kafin damina ta sauka manomi ya samu iri a hannunsa damina tana sauka ya tafi gona; sannan idan manomi ya noma a saya da farashi mai kyau.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: