Connect with us

MANYAN LABARAI

Masari Ya Ja Kunnen Masu Yi Wa Gidauniyar Dangote Makarkashiya

Published

on

Gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya yi gargadin cewa, gwamnatin jihar ta Katsina ba za ta lamunci sanya siyasa ko zagon kasa da makarkashiya ga tsarin shirin tallafa wa mata da Gidauniyar Dangote ke yi a fadin jihar ba.

Gwamnan ya bayayana hakan ne a lokacin da ya kira wani taro da shugabannin gargajiya, addini tare da ’yan siyasa daga Shiyyar Daura game da yadda za a rarraba kudaden da Gidauniyar ta Dangote ta bayar da tallafi.

Gwamnan, wanda ya yi magana ta bakin shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin jihar, Alhaji Muntari Lawal, ya yi gargadin cewa, dukkan wanda a ka kama da hannu a cikin cutar wadanda su ka amfana da shirin, ya yi kuka da kanshi.

Gwamna ya bayyana rashin jin dadinshi a kan rohoton da a ka samu na cewa wasu masu son kai a shiyyoyin Katsina da Funtua, wadanda ba su ne ya kamata su amfana da shirin tallafin ba, sun aikata son ransu.

Ya kuma ce, daga yanzu jami’an tsaro za su kama dukkan wanda a ka samu da laifin karbar wani kudi daga hannu matan da a ke bai wa tallafin.

Gwamna Masari ya bukaci dukkan matan da a ka tantance, su rika zuwa cibiyar da a ke biya ba tare da wani dan rakiya ba.

Ita ma yayin da ta ke magana, shugabar kwamitin da ke raba kudaden kuma babbar sakatariya a ma’aikatar kula da lafiya da safiyo, Hajiya Rayyanatu Lawal, ta yi magana a kan hanyoyin da a ka bi wajen zabo wadanda za a tallafa wa domin ganin shirin ya kankama ba tare da an cuci kowa ba, ta na mai cewa, sanin kowa ne kan irin yadda gwamnatin jihar ta dage, domin ganin wannan shirin ya yi wa dukkan al’ummar jihar nan amfani ba tare da wani son kai ba wanda har ma tuni shirin ya kankama bisa bin umarnin hukumomin da su ka tsara shirin.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: