Connect with us

JAKAR MAGORI

Matasa Biyu Sun Nutse A Kududdufin Jihar Ebonyi

Published

on

An sami fargici da tashin hankali a garin Afikpo da ke cikin karamar hukumar Afikpo ta Jihar Ebonyi, lokacin da wasu matasa guda biyu suka nutse a cikin kududdufin. Matasan masu suna Emmanuel Chiaha dan shekara 17 da kuma Christopher Chiaha mai shekaru 13, sun dai nutse a kududdufin ne lokacin da suka ziyarci yankin Ndibe Beach da ke cikin garin Afikpo. An dai bayar da rahoton cewa, matasan guda biyu sun bar gida ne da misalin karfe uku na yadda, inda suka bayyana wa iyayen su cewa za su je waje su yi wasa. Ba su dawo gida ba har lokacin da iyayensu suka fara neman su. Daga baya dai an gano gawarsu a cikin kududdufi. Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoton ba a san musabbabin mutuwarsu ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Ebonyi, DSP Odah Lobeth, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta bayyana cewa, mutuwar matasan ta zo ne ba zato ba tsammani. Ta kara da cewa, an ijiye gawarwakinsu a dakin ijiye gawarwaki da ke cikin asibiti.

Odah ta ce, “wani mutum mai suna Chiaha Madabuchi ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sandar yankin Afikpo ta arewa. Ya bayyana cewa, matasa guda biyu masu suna Chiaha Emmanuel dan shekara 17 da kuma Chiaha Christopher dan shekara 13 sun mutu a cikin kududdufi lokacin da su ka je yin wanka a yankin Ndibe Beach cikin garin Afikpo da misalin karfe uku na rana, bayan sun bar gida sun ce wa iyayensu za su je yin wasa a waje.

“’Yan sanda sun ziyarci kududdufin, inda suka dauki hortonan gawarwakin sannan suka ijiye gawarwakin a dakin ijiye gawarwaki da ke cikin asibiti. Sai dai ba a sami sauri a cikin jikinsu ba.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: