Connect with us

MAKALAR YAU

Matasalar Almajiranci: Mene Ne Mafita? (1)

Published

on

Kalmar almajiranci na da manufa guda biyu: wato tsarin koyar da yara karatun allo a wasu kasashe na Yammacin Afirka, musammamn a arewacin Najeriya, inda a kan tura su wasu garuruwa wajen malamai domin koyar da su ilimin Kur’ani. Daya manufar kuma ita ce ta yadda wadannan kananan yara ke yawace-yawace a lungu da sako na garuruwan da su ke karatu su na barar abinci.

Almajirci ya samo asali daga fadar Manzon Allah (SAW) lokacin da shahararren maruwaicin hadisin nan, wato Abu Hurairah, ya yi hijira daga garinsu ya zo ya tare a fadar annabi inda ya ke daukar karatu. Abu Hurairah ya kasance ba ya aikin komai idan banda zama a wannan majalisi ya na haddar hadisai.

Wannan dabi’a wadda ta faro tun zamanin annabi ta kasance ta watsu a sauran sassa inda daular musulunci ta mamaya, musamman a dogon zamanin da Musulmi su ka yi a Andalusiya (wato kasashen Spain da Portugal da ke Turai a yanzu) har na tsawon shekaru dari bakwai (700).

A wannan daula ne aka inganta wancan tsari na almajiranci domin ya zama hanya ta koyar da ilimi ga yayan talakawa ta yadda a ke tura su wajen malamai a makarantu da aka samar jikin kowanne masallaci.

A garin Cordoba, cibiyar wannan daula, tsarin tsangaya ya samo asali inda kowacce makaranta ke da babban malami kuma ake rarraba yara hurhudu a kowanne daki da za su rika daukar karatu.

Garuruwan Cordoba da Toledo sun kasance a wancan karni tamkar yadda a yanzu za ka ce biranen New York da London a ci gaba. A wancan zamani a lokacin da birnin Cordoba ke da dakunan karatu 70, da kuma gidajen wanka na al’umma kimanin 500, da manyan tituna wadanda, duk da cewa wancan lokacin ba’a gano kwalta ba, amma an dandabe su yadda su ke da fadi kuma an jejjera bishiyoyi a kowanne gefensu, sannan kana iya tafiya a kan wadanna tituna na tsawon mil goma da daddare saboda an kunna fitulun a-ci-balbal suna haskaka su har gari ya waye.

A daidai wannan lokaci da garin Cordoba ke da wannan ci gaba, idan ka tsallaka kogin Bahar Rum (Mediterranean) ka shiga turai, a kasar Faransa idan ka fito kofar gidanka, kwata ce zata kama ka har gwiwa. Sannan a birnin London idan kana yawo a titi sai kana lura saboda kar wata mata ta watso bola a kanka ko ma kashin da ta wanke na danta. A lokacin da Cordoba ke da dakunan wanka na al’umma kimanin dari biyar, hatta Sarauniyar Ingila ba ta wanka sai dai idan wata lalura ta rashin lafiya ta sa mai maganinta ya ce hanyar warakarta daga wannan cuta ita ce ta yi wanka. Turawa a lokacin sai su shekara ba su yi wanka ba.

A lokacin da Turai ke cikin wannan duhun kai, Musulmi a Andalusiya sun yi nisa wajen fassara littafan falsafa na Girkawa zuwa larabci. Harkar ilimi da ci gaban al’umma da ke wanzuwa a Analusiya ya sanya turawa sun fara tunanin ta yaya wadannan mutane daga Hamada a kan rakumi su ka sami sirrin gina daula irin wannan?

Kasancewar mahukunta a Andalusiya sun mai da hankali wajen bunkasa ilimi ta hanyar fassara littafan falsafa na Girkawa, sai turawa su ka yi amfani da wannan dama wajen tura matasa masu hazaka zuwa jami’o’i da dakunan karatu na daular su shiga aikin fassara tare da yi musu leken asiri.

Tarihi ya nuna cewa Shaihun malamin kirista, Peter The Venerable, ya zama tamkar gada wajen fassara rubuce-rubucen Musulmi a Andalusiya zuwa turanci, kuma shine wanda ya fara fassara Kurani da kansa zuwa wani yare na turai.

Turawa sun nemi a basu amsar sirrin nasara da ci gaban Musulmi a wancan zamani, kuma masana da su ka yi musu nazari da leken asiri sun bada rahoton cewa hakika Musulmi na da sirriku guda biyu, wato na farko shine Kuraninsu, wanda ya kawo musu ilimi da shari’a mai adalci wadda su ka dabbaka, sannan da wancan tsari na almajiranci karkashin tsangaya wanda a ka kirkiro a Andalusiya da ke baiwa al’umma gama-gari ilimi kuma ke jaddada bincike a jami’o’in Musulmi.

Wadannan abubuwa biyu, Kur’ani da Almajiranci, sune su ka kai daular musulunci a Andalusiya ta zarce kowacce daula ta zamaninta a tsarin mulki, ilimi, adalci, ci gaban tattalin arziki da tsaro. Turawa sun gamsu da wannan tsari na almajiranci dari bisa dari kuma sun sha alwashin kwaikwayar Musulmi ta hanyar daukar duk wani abu mai kyau da Kur’ani ya kawo ba tare da hadarin sun musulunta ba amma su dabbaka shi cikin tsarin rayuwarsu.

Don haka ne a yanzu duk irin tsare-tsare na manhaja da dabi’un masana a jami’o’in turai zaka samu cewa kwaikwayo ne kai tsaye daga jami’o’in Andalusiya a wancan lokaci. Hatta rigunan da ake sakawa wajen yaye dalibai (Academic gown) na kowanne irin digiri an kwaikwayo su ne daga alkyabbu wadanda mashahuran malaman andalusiya irinsu Ibn Rushid su ke sawa lokacin da su ke koyarwa a wadancan jami’o’ina Andalusiya. Tsarin Undergraduate, graduate, lecturer, professor, chair da sauransu duk sun samo asali daga tsari kolo, titibiri, gangaran, alaramma da a ka tsara tsangayu a Andalusiya.

Tsarin almajiranci a yammacin Afirka kuwa ya samo asali ne a wajajen karni na 11 lokacin da Al-Murabit (Almorabids) wadanda sakamakon nasarar daular Andalusiya su ma su ka tashi tsaye su ka kafa wata daular musulunci a kasashen magrib. Wannan daula ita kuma a nata tsaikon ta yi fadin kilomita dubu uku a kasashen kudu da arewacin Hamada. Wannan daula ce ta karya daular Ghana wadda burbushinta ya samar da daular Mali wadda a tsaikon ta Mansa Musa ya yi mulki.

Tafiyar Mansa Musa aikin hajji a shekarar 1324 ta kasance tafiya wadda ta shahara a tarihi ta kuma jawo hankalin turawa game da kasashen da ke Afirka kudu da Hamada. Wannan tafiya aikin hajji ta Mansa Musa, wadda ya tafi da mutane dubu sittin da bayi dubu goma sha biyu, saboda irin yawan arzikin da ya kwasa na zinari ya kuma rika rabarwa a hanyarsa sai da ya jawo karyewar tattalin arzikin kasashen da ya ratsa ta cikinsu har da Cairo, abinda ya jawo ja-bayan tattalin arzikin kasashen na kusan shekaru goma bayan wucewarsa.

Karkashin wanna daula ta Mali Wangarawa, wadanda ana iya kiransu fataken malamai, sun iso birnin Kano lokacin Sarkin Kano Yaji a karni na 13. Su ne su ka fara kawo musulunci kasar Hausa da kuma tsarin tsangaya. Bayan shekaru Dari da zuwan wangarawa, shi kuma Al-Maghili, wanda ya taso daga cikin wancan daula ta Almorabid, ya isa Kano a karni na 14 lokacin mulkin Sarki Muhammadu Rumfa.

Al-Maghili ya rubutawa Rumfa littafin da ya kira “Taj al-din fi ma yajib ‘ala l-muluk” kuma ya taimaka wajen habaka tsarin tsangaya da almajiranci a birnin Kano. Wannan tsari na tsangaya da ya shigo kasar hausa ya zama tamkar wata hanya ta farko ta yada ilimi tsakanin al’umma. Wannan tsari shi ya samar da rumbun samar da malamai, limamai da masu wa’azi wadanda ke karantar da yayan talakawa ilimin karatun Kur’ani kamar yadda asalinsa ya ke a daular Andalusiya.

Tsari ne da ba ilimi kawai ya ke koyarwa ba har da girmama na gaba, juriya da dauriya da biyayya da tarbiyya. Shekaru kusan dari hudu da zuwan Al Maghili da jaddada tsarin tsangaya a kasar hausa, Shehu Usmanu Danfodiyo kan sa ya fito ta wannan tsari na almajirci inda ya kaddamar da jihadi akan sarakunan habe saboda mulkin zalunci, kuma ya kafa daular musulunci ta Usmaniyya a farkon karni na 19.

Daular Usmaniyya ta samar da tsari na adalci da zaman lafiya da ci gaba a yankin Afirka ta yamma sama da tsawon karni guda. Kuma ita ce ta inganta tsarin ajami na larabci da tsarin tsangaya na makarantun allo wanda ke baiwa dalibai damar samun ilimi su zama malaman koyarwa ko limamai ko masu wa’azi a kasar hausa, tare da zama babbar hanyar ta tsarin ilimintarwa da kuma tarbiyyantar da al’umma.

Bayan zuwan turawan mulki mallaka tare da murkushe daular Dan Fodiyo, tsarin almajiranci a karkashin tsangayu sai ya fara daukar sabon salo saboda an kwace karfin ikon sarakunan gargajiya wanda ya raunana tsarin. Sarakuna sun kasance iyaye masu kula da tsarin a baya saboda su ke bawa malamai filayen noma wadanda almajirai ke nomawa su samar da abincin da za su ci tsawon shekara, sannan Sarakuna har ila yau su ke tattara zakka wadda ake baiwa malamai da almajiransu.

Haka nan iyayen yara duk shekara su na kawo nasu tallafin na abincin da su ka noma ga malaman yayansu da ke tsangayu. Rashin wannan ginshikin tallafi ya bar malamai ba su da zabi wanda ya wuce su tura yaran bara domin samun abinci. A wannan gaba ne bara ta cuso kai cikin tsarin almajirci wanda watakila da gangan turawa su ka kirkiri wannan tsari domin gurgunta tasirin almajiranci a yammacin Afirka sanin yadda mahimmancinsa ya kasance a Andalusiya har su ka kwaikwaya.

A takaice wannan shine tarihin yadda almajirci ya samo asali tare da irin tasirinsa, ba a rayuwar Musulmi ba kawai ba, har ma ga daukacin al’ummar duniya domin kamar yadda na fada a baya duk tsarin karatu na jami’o’I a yanzu ya kwaikwayi tsarin tsangaya na farko daga Andalusiya.

Amma abin takaici shine almajiranci ya balbalce a yanzu, kuma a bayyane ya ke cewa almajiranci a yau sabanin yadda aka san shi a baya ne, domin a da ya kasance babbar hanyar ilimintar da al’umma da tarbiyyantar da ita amma yanzu ya zama babbar hanyar tsunduma cikin jahilci da rashin tarbiyya…..

 

Za mu cigaba a mako mai zuwa in sha Allah.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: