Connect with us

JAKAR MAGORI

Matashi Ya Halaka Karuwa A Jihar Legas

Published

on

Wani matashi dan shekara 28 ya shiga hannu, bisa laifin sokar wata karuwa har lahira tare da raunata mutum biyu wadanda su ka yi kokarin hana shi gudu lokacin da ya aikata laifin. Lamarin dai ya faru ne a wani otal da ke kan titin Atan cikin yankin Surulere ta Jihar Legas, in ji ‘yan sanda. Wanda a ke zargin mai suna Babatunde Damilare, an bayyana shi a matsayin wanda ya ke halartar wannan otal ko da yaushi, ya dai farmaki wata karuwa mai suna Elochukwu da wuka, a lokacin da su ka samu rashin jituwan abinda zai biyu kudin kwanan da ya yi da ita ranar Juma’a. “Shi dai Babatunde ya na yawan zuwa wannan otal, ya daba mata wukan da a ke yanka ganyenyaki.

Haka kuma ya farmaki wasu mutum biyu wadanda su ka yi yunkurin hana shi gudu lokacin da ya aikata wannan laifi. Dukkan su dai an garza da su asibiti, inda likita ya tabbatar da mutuwar matar, yayin da mutum biyun ke cikin mayuyacin hali,” in ji ‘yan sanda.

‘Yan sanda sun bayyana cewa, sun dai damke Babatunde ne bisa laifin kisan kai, inda a ka mika shi sashen rundunar ‘yan sanda masu binciken manyen laifuka da ke Panti cikin garin Yaba.

Wata karuwa a wannan otal ne ta kai rahoton lamarin, inda ta ke cewa, “Babatunde bai da niyyan biyan karuwan kudinta bayan ya kammala lalata da ita,” wannan ba shi ne karo na farko ba da mutumin ya ke kin biyan kawuwan kudinsu a otal din. Ta ce, da ma can Babatunde ya na shirin aikata wannan mummunan aiki.

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Bala Elkana ya bayyana cewa, lamarin ya faruwu ne ranar Juma’a da misalin karfe 11 na dare. Ya kara da cewa, a wannan rana ne ‘yan sanda daga yankin Surulere su ka samu rahoton kashe karuwa mai suna Elochukwu, wacce abokin huldanta mai suna Babatunde Damilare ya daba mata wuka lokacin da su ke fada sakamakon biyanta kudin kwananta. “Lokacin wannan lamari, Babatunde Damilare ya caka wa Elochukwu wuka a wuyarta da dama, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta nan take. “Tawagar ‘yan sanda da ke yankin Surulere wanda CSP Adebayo Adeoya ya ke jagoranta sun samu nasarar damke wanda a ke zargi. An dai ijiye gawar marigayyar a dakin ijiye gawarwaki da ke cikin asibiti. Za a gurfanar da wanda a ke zargi a gaban kotu idan a ka kammala bincike,” in ji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: