Connect with us

RAHOTANNI

Miyetti Allah Ta Zabi Sabbin Shugabanninta A Neja

Published

on

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breaders ta Najeriya (MACBAN)  reshen jihar Neja ta zabi sabbin shugabanninta domin samar da sabon sauyi da cigaban kungiyar, tunda farko a bayaninsa mataimakin shugaban kungiyar ( MACBAN) ta kasa, Alhaji Husaini Bosso ya ce zaben sabbin shugabannin ya zo ne a daidai da lokacin da kungiyar ke yunkurin samar da sabbin tsare tsare da za su zo daidai da yadda abubuwa ke tafiya a yanzu na rashin tsaro da wayar da kan matasa illar rashin tsaro da abinda ke kawo koma baya a cikin al’umma.

Husaini Bosso ya jawo hankalin sabbin shugabannin da su samar da tsarin da zai iya tafiya da kowa domin dukkanin kabilun Fulani suna da rawar takawa wajen samun cigaba da bunkasar tattalin arzikin kasa ta yadda dole sai an samu zaman lafiya da fahimtar juna sannan ne za a iya cin ma wannan burin.

Saboda haka tsakanin sabon shugaban, Alhaji Muhammad Abubakar Sadik da tsohon shugaba Alhaji Ardo Adamu Kaduna tamkar da da uba ne, dan haka dukkanin bangarorin Fulani da su bada hadin kai da goyon baya ga wannan sabon shugabancin, don cigaban al’ummar Fulani da kawo sauyi mai anfani musamman ga matasa da mata dan samar da kyakkyawar al’umma mai anfani a kasa.

Da ya ke bayani, sabon shugaban, Alhaji Muhammad Abubakar Sadik, yace a shirye ya ke wajen hada kai da dukkanin bangarori da sauran kungiyoyin da ke yunkurin kabilun Fulani dan samun cigaba da zaman lafiya a kasa.

Yanzu haka ba tare da bata lokaci ba za mu fara rangadi dan tattauna wa da dukkanin bangarori da shugabannin Fulani dan hada kai da yin aiki tare ta yadda zamu samu damar hada kai dan fuskantar kalubalen da ke gaban mu.

A yanzu kowa yasan halin da kasar nan ke ciki na rashin tsaro, za mu bullo da tsare-tsaren da kowa zai bada gudunmawa wajen wayar da kan al’ummar mu da samar da kyakkyawar tsarin da zai inganta rayuwar mata da matasa musamman dan samar da al’umma ta gari.

Alhaji Ardo Adamu Kaduna, shi ne tsohon shugaban kungiyar, ya zargi shugabancin kungiyar ta kasa da yunkurin rarrabawa kawunan kabilun Fulani ta hanyar shawartar sa da ya sake neman shugabancin kungiyar karo na biyu duba da tsarin kungiyar ta ba shi wannan damar amma daga bi sani ta tsame shi bayan ta tabbatar ya sayi fom dan sake gwada kunjin shi na neman shugabancin inda ta shelanta nada Abubakar Sadik a matsayin sabon shugaban kungiyar ta jihar.

Ardo Kaduna yace hanyar da uwar kungiyar ta kasa ta bullo da shi ba mai bullewa ba ne, domin da ta san tana da wannan kudurin bai kamata ta sanya shin yin takara karo na biyu ba, dan wannan bai cikin tsarin kungiyar wannan hanya ce ta yaudara da ha’inci. Ba a bani damar zantawa da jama’ata ba, sai aka ware ni, ni kawai aka ce min in janye shugabannin kungiya sun zartas da nada Sadik a matsayin shugaba na jiha wanda wannan ba daidai ba ne.

Lokacin da shugaban kungiyar ya nemi sake dawo wa a matsayin shugaba na kasa karo na biyu, ban da lafiya amma haka muka tashi muka ba shi goyon baya, ban da tunanin sake neman shugabancin karo na biyu amma shugabannin kungiyar ta kasa suka tirsasa ni akan lallai sai nemi takara ta biyu, bayan na amince kuma na sayi fom aka bullo min da wannan yaudarar, wanda Ina kallon sa a matsayin wani yunkuri na assasa kabilanci da rarraba kawunan ‘yayan Fulani domin hanya ce a ka dauko da ba za ta haifar da da mai ido ga Miyetti Allah Cattle Breaders ba.

Yanzu a cikin shugabannin jiha da na yi aiki tare da su, ni kadai aka tsame a ka ce idan aje shugabancin, amma sauran abokan aiki na duk an mayar da su, in ma su shugabannin na kasa na yi masu laifi ne ai sai su zaunar da ni,  su fada min laifina amma ba wai su yi min irin wannan hukunci ba, idan wannan kungiyar ta bargawa ce ba na al’ummar Fulani ba, sai su fito su fada mana, wannan tafiyar ba tai kama da Miyetti Allah ba, domin ita Miyetti Allah ta kowace amma ba wai a ware wasu kabilun Fulani a mayar da su saniyar ware kuma a ce dole su amince da wannan tafiyar ba.

Amma an zabi gida daya, daga kane sai wa da da kuma an ce wai su ne za su jagoran sauran kabilun Fulani. Wannan kabilanci ne kuma ba hanya ce ta hadin kai ba, domin duk abinda wata kabila ta bayar na gudunmawar cigaban wannan kungiya a baya mun bayar amma yau an ware mu ana kokarin mayar da mu saniyar ware, wanda wannan tsarin ya sabawa zamantakewar al’umma kuma hanya ce da aka bullo da ita dan rarraba kan kabilun Fulani makiyaya.

Saboda haka ban amince da wannan tsarin ba, kuma ba mu gamsu da shi ba saboda ba a bi hanyar da ta dace ba wajen zartas da shi ba, an nuna mana fin karfi kuma an dan ne mu a wannan tsarin da a ka bullo da shi yanzu.

Alhaji Isma’ila Rabe, daya daga cikin masu ruwa da tsaki na kungiyar ya janyo hankalin dukkanin bangarori da su hada kai su yi aiki tare, domin dukkanin manufofin su daya ne shi ne hadin kai, cigaban al’ummar Fulani.

Maganar zabe kuma ai an yi zabe, domin tsarin tafiyar da kungiyar MACBAN tana da tsare tsaren zabe kuma da shi a ka yi anfani wajen samar da sabon shugabancin.

Dan haka ina jawo hankalin sabon shugabancin kungiyar nan da tayi aiki kafada da kafada da kungiyar ‘yan sa kai na Miyetti Allah, domin hatta jami’an tsaro sun yaba da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen farautar bata gari, saboda ‘yansa kai na da muhimmanci sosai a wannan tafiyar.

Babban burin mu shi ne a samar da kudurce kudurce masu anfani da zasu anfani al’umma da kasa baki daya wajen samun zaman lafiya da cigaban tattalin arzikin kasa.

Alhaji Muhammad Abubakar Sadik shi ne mataimakin jami’in hulda da jama’a ta kungiyar a matakin kasa kuma tsohon darakta a hukumar ilmantar da ‘yayan makiyaya NOMADIC reshen jihar Neja, kwararren dan jarida shugaban sashen labarai na gidan radiyon jihar Neja.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: