Connect with us

LABARAI

NIS Ta Ja Hankalin Jami’anta Kan Rigakafin Kamuwa Da Cututtuka

Published

on

Babban Kwanturolan hukumar Shige da fice ta kasa, Muhammad Babandede MFR, ya umurci dukkanin daraktocin sassan hukumar musamman wadabda da suke kan iyakokin shigowa kasar nan, kamar tashoshin Jiragen sama da tashoshin Jiragen ruwa da ma kan iyakoki na kasa, da su dauki matakan kare kansu daga cudanya da bakin da suke shigowa kasar nan domin rigakafin kamuwa da duk wata cuta.

Cikin sanarwar manema labarai wacce babban jami’in hulda da jama’a na hukumar DCI Sunday James ya fitar, ta yi bayanin cewa, Kwanturolan hukumar da ke shiyyar Jihar Ogun, Doris Braimah, wadda ta shelanta wannan umurnin a kan iyakar kasar nan da ke Idioroko, ta shawarci jami’an hukumar da su guji yin sakaci a kan duk wata cuta da ta shafi tari, zazzabi ko ta samun matsala a wajen numfashi, wadanda duk alamomi ne na wasu cutuka masu wuyar sha’ani.

Ta kuma karfafe su da su zama masu kiyayewa da duk wani bakon da ke shigowa cikkin kasar nan da kuma kayan bakin, ta hanyar sanya matakan kariya na safunan hannayen su da kuma toshe hancin su ba kuma tare da nuna kyamata ba. Sannan su rika hada kai da jami’an lafiya da suke a kan iyakokin domin hana duk wata bakuwar cuta samun kafar shigowa cikin kasar nan.

Kan iyakar kasar nan da ke Idioroko, daya ne daga cikin manyan kan iyakokin kasar nan da muke da iyaka da kasar Benin, wacce kuma ake samun kwararowar baki ta cikinta masu yawa. Braimah ta raba wa jami’an hukumar ta NIS da ma na sauran hukumomin da suke aiki a tare da ita da safunan hannu da abin rufe fuska domin su rika amfani da su a kan iyakar ta Idioroko.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: