Connect with us

WASANNI

Paul Ntep Ya Bar Kungiyar Wolsburg

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Wolsburg ta kasar Jamus da dan kwallon tawagar Kamaru Paul-Georges Ntep sun amince kowa ya kama gabansa sakamakon halin rashin jituwa da bangarorin suka samu kansu

Dan wasan mai shekara 27, bai samu damar buga wasa akai-akai ba a Jamus, inda ya buga karawa 19 a Wolsburg tun da ya koma kungiyar a shekara ta 2017 daga kungiyar kwallon kafa ta Rennes dake kasar Faransa.

Ntep ya buga wasannin aro a zango na biyu a kakar wasa ta 2018/19 a kungiyar Saint-Etienne ta Faransa haka kuma a kakar nan ya buga wasan aro a Turkiya a tare da kungiyar Kayserispor wadda ta amince za ta saye shi, amma matsalar rashin kudi ya sa aka hakura da cinikin.

Yanzu haka Ntep na neman kungiyar da zai buga wa kwallon kafa domin ya samu gurbin buga wa tawagar Kamaru gasar cin kofin nahiyar Afirka da za ta karbi bakunci a shekara ta 2021 mai kamawa.

Dan wasan ya buga wa matasan Faransa masu kasa da shekaru har mataki hudu tun daga ‘yan 18 zuwa 21, ya kuma buga wa babbar tawagar wasannin sada zumunci biyu, daga baya ya koma yi wa Kamaru wasa a shekarar 2018.

Tun da ya amince da buga wa Kamaru kwallon kafa ya ci kofi hudu a Indomitable Lions ya kuma buga wasa biyu karkashin Clarence Seedorf kafin daga baya kasar ta kori mai koyarwar tata.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: