Connect with us

WASANNI

PSG Ta Lallasa Dijon Da Ci 6 Da 1

Published

on

Kungiyar PSG dake Faransa ta Lallasa kungiyar kwallon kafa ta Dijon a gasar kofin Faransa ta ‘French Cup,’ wanda ya gudana a ranar Laraba. Inda wasan aka tashi da ci 6 da 1.

Pablo Sarabia ta PSG shi ne ya kwallo biyu ma kungiyarsa. Dijon sun fara fuskantar matsala ne tun lokacin da dan wasanta Wesley Lautoa ya ci kansu ta hanyar sanya kwallon a ragarsu.

Sai dai kuma Mounir Chouiar na Dijon ya rama kwallon a minti na 12, inda kafin tafiya hutun rabin lokacin kuma Kylian Mbappe ya rama.

Daga dawo wa hutun rabin lokaci da minti biyar, Thiago Silva ya ci kwallo guda, inda kuma Sarabia shima ya ci a minti 56. Dan wasan tsaron baya na Dijon Senou Coulibaly shima ya zura wa kansu kwallo a gida a minti na 86, kafin gab da tashi Sarabia ya kara kwallo guda.

A gasar Ligue 1 kuwa na Faransar, kungiyar ta Dijon it ace ta 17.

Yanzu haka PSG din ta tafi wasan gab da na karshe a gasar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: