Connect with us

WASANNI

Real Madrid Za Ta Bada Isco Da Kudi Don Sayen Pogba

Published

on

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta shirya sallama dan wasanta na tsakiya, Isco, sannan ta cika kudi domin daukar dan wasan tsakiyar Manchester United, Paul Pogba.

Tun bayan komawar Zidane kungiyar a karo na biyu yayi alkawarin zai sayi dan kwallon domin yanason suyi aimi tare a Real Madrid kuma shima dan wasan ya bayyana burinsa na bugawa kungiyar wasa.

Real Madrid zata sake komawa domin taya dan wasan a kakar wasa mai zuwa bayan da suka taya shi a kakar data gabata amma Manchester United tayi fatali da tayin na Real Madrid kuma dan wasan ya cigaba da zama a Ingila.

Manchester United dai tana neman zunzurutun kudi har fam miliyan 148 sai dai Real Madrid zata saka dan wasa Idco acikin cinikin domin ta samu saukin adadin kudin da zata biya idan an amince da cinikin.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta dade tana fatan sayan dan wasa Isco wanda gaba daya a wannan kakar wasanni tara na laliga Zidane ya fara da dan wasan kuma shima yana fatan barin kungiyar a kakar wasa mai zuwa

Shima dan wasa Pogba yana fama da ciwo a wannan kakar inda har yanzu wasanni takwas ya bugawa kungiyar a gasar firimiya kuma sayan dan wasa Bruno Fernandez zai sake sawa Manchester United ta sayar da Pogba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: