Connect with us

LABARAI

Rundunar Tsaro Ta NSCDC Za Ta Fara Cafke Masu Sayar Da Layukan Waya Masu Rajista A Jigawa

Published

on

Hukumar tsaro ta NSCDC reshen jihar Jigawa ta sanya hannun yarjejeniya da hukumar sadarwa ta kasa wato NCC domin magance yaduwar layukan waya masu rijista a jihar.

Adamu Shehu, Kakakin hukumar NSCDC din shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a garin Dutse a ranar Laraba, inda ya ce sun dauki wannan matakin ne domin magance matsalar amfani da layukan waya wadanda suke dauke da bayanan boge.

Shehu ya yi gargadin cewa hukumar ta su nan ba da jimawa ba za su fara cafke masu siyar da irin wadannan layukan wata masu rijista a fadin jihar.

Hukumar ta NSCDC ta ce duk da gargadi da suka rika yi, kamu da gurfanar da wadanda aka samu da hannu a irin wannan hali, amma hukumar ta su ta gano akwai wadanda suka ci gaba da siyar da wadannan layuka a jihar.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: