Connect with us

LABARAI

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kama ‘Yan Kungiyar Asiri Biyar A Adamawa

Published

on

Jami’an rundunar ‘yan sanda sun kama mutum biyar, wadanda su ke zargi da kasancewa ‘yan kungiyar asiri ne a ranar Talata a jihar Adamawa.

Cikin wata sanarwa ga manema labarai, jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Suleiman Nguroji, ya ce rundunar ta kame mutanen ne a jami’a mallakin jihar (wato ADSU) da ke Mubi.

DSP Nguroji ya ce, rundunar ta cafke mutanen  biyar ne ranar Litinin a garin Mubi biyo bayan zargin kasancewarsu ’ya’yan wata kungiyar asiri.

Ya ce, “kame su ya biyo bayan zargin su da kasancewa ’ya’yan kungiyar asiri ta Neo Black da Black Arrows cult.

“Sun fara kai wa daliban da ba su san hawa ba ba su san sauka ba hari da raunata su ta bangarori daban-daban.

Ya cigaba da cewa, “jami’an ‘yan sanda sun samu bindigogi kirar pistol guda biyu, adduna, wukake, zabbuna da layu a hanunsu” in ji Nguroji.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan ya shawarci jama’a, musamman iyaye da jami’ai ko shugabannin makarantu, da su mayar da hankali da lura da inda su ke, inda ya kara da cewa, su kuma sanar da rundunar ’yan sandan duk yanayin da ba su gamsu da shi ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: