Connect with us

RIGAR 'YANCI

Sabon Shugaban Hukumar Alhazan Katsina Zai Fidda Kunya – Abdu Dutsinma

Published

on

An lura da cewa, sabon shugaban gudanarwar hukumar kula da jin dadin alhazai na Jihar Katsina, wanda a ka nada kwanan nan zai bai wa marada kunya a yayin sauke nauyin aikin shi sakamakon gogewa da kwarewar aikin da ya ke da su.

Tsohon daraktan sashen ilimi da walwalar jama’a Abdu Bawa Dutsinma ya bayyana hakan ga manema labarai a Katsina.

Kamar yadda yace ba’a taba kama Alh. Suleiman Nuhu Kuki da laifi ba a lokacin daya kwashe yana aiki tun daga tsohuwar jihar Kaduna har zuwa jihar Katsina shekaru 33 da suka wuce.

Mal. Abdu Bawa yace sabon shugaban hukumar alhazai ta jihar Katsina zai nuna halin dattako da hakuri da juriya wajan gudanar da ayyukan hukumar.

Ya yi nuni da cewa a lokacin da ya ke shugaban hukumar SUBEB ta jihar Katsina ya inganta malaman makarantar firamare da sauran ma’aikatan.

Haka nan kuma Mal. Abdu Bawa Dutsinma yace a lokacin da Alh. Suleiman Nuhu yake jami’in dake kula da gidan jihar Katsina dake Kaduna ya tabbatar da cewa dukan baki sun samu kulawar da suke bukata ba tare da nuna banbanci ba.

A yayin da ya ke bukatar sabon shugaban hukumar jindadin alhazai ta jihar Katsina daya cigaba da gudanar da ayyukan alheri da ake sanshi dasu Mal. Abdu Bawa ya kuma yi addu’a Allah ya yi masa jagoranci.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: