Connect with us

RIGAR 'YANCI

Sanatoci Sun Gayyaci Kamfanin Kwangila Saboda Asarar Rayuka A Hanyar Kaduna-Kano

Published

on

Kwamitin Sanatoci mai kula da ayyukkan shinfida hanyoyin mota na kasar nan sun koka kan irin yadda mutane 48 suka mutu a hanyar Kaduna- Kano a cikin kwanaki kalilan. Saboda haka sun aike wa kamfanin da ke aikin kwangilar  hanyar goron gayyata kan irin yadda aikin nasu ke tafiyar hawainiya.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban kwamitin, Sanata Muhammadu Adamu Aliero yayin da ya jagoranci tawagar kwamitin Sanatocin masu kula da ayyukkan shimfida hanyoyin mota na kasar nan a fadar gwamnatin jihar Kano a lokacin da suka ziyararci Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Gunduje a Kano.

Ya ce, “bayyana wa gwamnatin Kano cewa kwamitinsa ba za su amince da yadda kamfanonin da ke shimfida ayyakkan hanyoyi a kasar nan ke yi, musamman wadanda ke aikin shimfida hanya daga Abuja-Kaduna zuwa Kano. Don haka mun aike wa kamfanin goron gayyata don yin bayanin abin da ke faruwa da aikin hanyar”.

Haka kuma ya kara da bayyana wa Gwamnan cewa, “mun kawo ziyarar aikin ne a jihar Kano domin mu ga irin yadda kamfanonin da aka baiwa ayyukkan ke gudanar da ayyukkansu. Wanda yana daya daga cikin ayyukkan da Sanatocin ke kula da shi kamar yadda yake a dokar kundin tsarin mulkin kasar nan.”

A karshe Sanata Adamu Aliero ya gode wa Gwamnatin jihar ta Kano a kan irin goyon bayan da ta ke ba Majalisar Dattawan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: