Connect with us

LABARAI

Sun Kone Shi Kurmus Saboda Ya Saci Kaza

Published

on

Taron fusatattun jama’a sun kone wani matashi mai suna Victor kurmus a jijjifin shekaranjiya a Unguwar Ekpo Edem, da ke karamar hukumar Kalaba ta Kudu, a bisa zargin sa da satar Kaza.

Lamarin ya auku ne a daidai mahadar nan ta, Abitu Avenue ta Ekpo Edem daura da Cocin Living Faith Church da misalin karfe 5 na safiya.

Wani wanda lamarin ya auku a kan idonsa mai suna, George Asukuo, cewa ya yi, “Wanda aka kone din ya saba da yin ‘yan sace-sace kamar na batiran mota, Janareto, dabbobi har da Kajin makwabta, alhalin duk mutane sun san shi da hakan.

“Matashin bai san cewa duk makwabta sun gano shi ba. duk da cewa a shekarar bara da ‘yan banga suka kama shi sun yi masa gargadin karshe, wanda kuma bai ji wannan gargadin ba.

“Da sassafen ranar sai ga shi ya sake zuwa domin ya saci wasu kajin, amma sai kajin suka fara kokawa, wanda hakan ne ya janyo hankulan masu kajin suka gane cewa wani ya shiga wajen kajin.

“Nan da nan sai mutanan suka yi kuwwa har jama’a suka taru suka kewaye shi, ko da aka damke shi da misalin karfe 4 na asubahin, sai mutanan suka ki yarda su rabu da shi a wannan karon, ba kuma tare da jimawa ba ne sai suka fara dukan sa, nan nan ma sai suka kyasta masa wuta a bisa kazar da ya sata,” in ji Asukuo.

A lokacin da wakilinmu ya tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar, ASP Irene Ugbo, wanda ya tabbatar da aukuwan lamarin, ya kara da cewa abin takaici ne yanda al’umma suka dauki matakin aiwatar da irin wannan danyan hukuncin.

Irene ya gargadi al’umma da su guji daukan doka a hannun su, a maimakon hakan kamata ya yi su danka wanda suke tuhuman a hannun ‘yan sanda.

“Ba wai muna goyon bayan masu aikata laifi ne a kan munanan ayyukan da suke aikatawa ba, amma ya zama tilas mutane su fahimci cewa zaytas da doka da hannun su a kan duk wanda suke zargi da aikata laifi wannan danyan hukunci ne, kamata ya yi su gabatar da shi a bincike shi da kyau a kuma hukunta shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: