Connect with us

JAKAR MAGORI

Ta Lakada Wa Mijinta Duka Saboda Ya Kasa Yi Ma Ta Ciki

Published

on

Kotun Ejigbo ta garkame wata matar aure mai suna Misis Chinwendu Chi ‘yar shekara 32 da haihuwa a gidan yari bisa laifin lakada wa mijinta mai suna Okechukwu Chita dukan kawo wuka a gidansu da ke kan titin Alhaji Agbeke da ke yanakin Ago-Okota cikin garin Isolo, saboda ya kasa yi mata ciki. Chinwendu ta bayyana cewa, sun yi aure da mijinta ne tun shekarun da suka gabata, amma ya kasa yi mata ciki, sannan ya gaza nuna wani kokari a kan samun yaro.

An bayyana cewa, Chinwendu ta fara kai wa mijinta farmaki ne tun a shekarar 2018, bisa yadda mijin Okechukwu yake jin tsoron ta. ‘Yan sandan yankin Ago Palace sun shiga cikin lamarin, wannan ya sa rikicin bai yi kamari ba.

Ta bayyana cewa, ta kulle mijinta a daki a ranar 22 ga watan Disambar shekarar 2019, inda ta farmake shi da cokali mai yatsu a kansa da fuskansa wanda ya yi sanadiyyar ji masa rauni. Ta yi masa baraza kan daukar rayuwarsa, inda ta amshi kudi naira 650,000 a hannun mijinta. An bayyana cewa, shi dai Okechukwu, dan asalin Jihar Anambra ce, ya auri Chinwendu daga Jihar Abiya a shekarun da suka gabata, sai dai har yanzau ma’auratan ba su sami yaro ba tun da suka yi aure, shi dai Okechukwu dan kasuwa ne. ba zato ba zammani matan ta maida wannan lamari a kan Okechukwu. Ta fada wa ‘yan sandan yankin Ago za ta ci gaba da dukan sa matukar ya kasa yi mata ciki.

A ranar Litinin din da ta gabata, Chinwendu ta lakada wa Okechukwu dukan kawo wuka, inda ya kai wa ‘yan sanda rahoton lamarin. An bayar da rahoton cewa, ta farmaki wata jami’ar ‘yar sanda wacce ta yi kokarin kai ta zuwa ofishin ‘yan sanda. Daga baya dai ‘yan sanda sun sami nasarar damke ta, inda suka gurfanar da ita a gaban kotun Ejigbo, bisa laifin farmakar mijinta da kuma ‘yar sanda.

Sai dai ta musanta laifin da ake tuhumar ta da shi.

Lauya mai gabatar da kara Supol Kenneth Asibor, ya bukaci kotu ta dage sauraron wannan kara domin bai wa ‘yan sanda damar gudanar da binciken musabbabin da ya sa matar ta aikata wannan laifi.

Alkali mai shari’a Mista Teslim Shomade, ya bayar da belin wacce ake tuhuma kan kudi na naira 700,000 tare da mutum biyu masu tsaya mata. Alkali ya bayar da umurnin a ci gaba da garkame ta a gidan yari har sai ta cika saruddan beli, yayin da aka dage sauraron wannan kara har sai zuwa ranar 11 ga watan 2020.

L


Advertisement

labarai

%d bloggers like this: