Connect with us

LABARAI

Tofa Yawu A Al’aurar Mace Na Iya Zama Hadari – Likita

Published

on

Wani kwararren Likita, Dakta Kolade Johnson, ya yi gargadi a bisa hadarin da ke tattare da yin amfani da yawu, domin samun saukin yin jima’i.

Kolade Johnson, wanda ke aiki a wani shahararren asibitin kwararru mai zaman kansa, ya fadi hakan ne a ranar Laraba a Ilorin, ya ke cewa a duk lokacin da mutum ya tofa yawun bakinsa wanda akwai wani ciwo a cikin bakin nashi a al’aurar mace, domin ya sami saukin yin jima’i, nan take macen za ta iya kamuwa da wata cutar a cikin al’aurarta.

Ya ce, cutar da ka iya samo asali daga yawun bakin na shi da ya sanya ko ya tofa domin samun saukin yin jima’in sun hada da cutukan da ke iya kama al’aurar mata kamar su, cutar Papilo, Syphilis, Chlamydia, da ma gwanoriya, da dai sauran su.

Kwararren Likitan ya ce, lamarin zai fi ma kazanta ne ga matan domin yawun bakin mutum yana lalata al’aurar mace duk da kewayenyen al’aurar ya kuma haifar mata da hanyar kamuwa da wasu cutukan.

“Sannan kuma, Yawun ma ba zai bayar da natijar saukin da ma ake son cimmawa ba, domin babu wuya da tofa shi ne sai kuma ya bushe cikin sauki.

“Hakanan kuma, idan wanda ya tofa yawun yana da warin baki, hakan zai iya sanya wa al’aurar macen ya kamu da wari, ya kuma rika fitar da warin.

“Don haka, sai Likitan ya bayar da shawarar hanya mafi sauki domin samun cikakken jin dadi da kuma sauki a lokacin jima’in shi ne a rika gabatar da wasanni har a kamu da sha’awa gabanin fara ainihin jima’in.

“In kuma har ba a samu yin hakan ba, to kamata ya yi a nemi tsaftataccen man shafawa mai maiko wanda Likitoci suka amince da shi, ba kuma irin wanda masu kemist din kafada su ke siyar da shi ba barkatai,” in ji Johnson.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: